Gwamna Inuwa ya yi alhinin rasuwar tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOlARI , Gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Alhaji Ibrahim El-Hassan Kwami, wanda aka fi sani da Sarkin Sudan na Kwami, bayan gajeruwar rashin lafiya.

A cikin saƙon ta’aziyya da darakta janar na harkokin yaɗa labarai na gidan gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga Jihar Gombe da ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce marigayi Ibrahim El-Hassan Kwami ya kasance gogaggen jami’in gwamnati kuma mutum mai kishin ci gaban al’umma, wanda ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a fannoni daban-daban na hidimar jama’a.

Ya tuna da irin gudunmawar da marigayin ya bayar yayin da yake riƙe da muƙamin kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Gombe, inda ya nuna ƙwarewa, sadaukarwa da nagarta wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

Gwamnan ya kuma yabawa irin rawar da marigayin ya taka a hukumar tara haraji ta tarayya, wadda yanzu ake kira hukumar tara haraji ta ƙasa, inda ya yi aiki har zuwa matakin babban jami’i, tare da nuna bajinta a fannonin kuɗi da gudanarwa.

Ya ce rasuwar Alhaji Ibrahim El-Hassan Kwami ta bar babban giɓi ga iyalansa, al’ummar Kwami, Jihar Gombe da kuma Najeriya baki ɗaya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, shugabanni da ma’aikatan hukumar tara haraji ta ƙasa, al’ummar Kwami, da daukacin abokai da masoyan marigayin.

Ya kuma yi addu’ar Allah maɗaukakin sarki ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa da duk masu alhinin haƙurin jure wannan babban rashi.

By ukarofi

Leave a Reply