Gwamna Lawal ya naɗa Aminu Atiku a matsayin sabon sarkin Zurmi na 21

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da naɗa Alhaji Aminu Atiku a matsayin sabon Sarkin Zamfaran Zurmi, bayan rasuwar tsohon sarkin.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin daga ofishin sakataren Gwamnatin Jihar da ke Gusau, Gwamna Dauda Lawal ya amince da naɗin bayan shawarwari masu kyau daga majalisar ƙoli ta masu naɗa sarki a masarautar ta Zurmi.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya ce an yi naɗin ne bisa ga al’adu, da kuma dokokin da suka dace na jihar.

Alhaji Aminu Atiku ya hau karagar mulki a matsayin Sarkin Zamfaran Zurmi na 21.

Ya gaji Mai Martaba, Alhaji Bello Suleiman, wanda ya rasu a ranar 31 ga Agusta, 2026.

Har zuwa lokacin naɗinsa, sabon Sarkin yana riƙe da sarautar gargajiya ta Dan Galadiman Zurmi.

Shi ne babban ɗan Sarkin Zurmi na 19, marigayi Mai Martaba, Alhaji Atiku Abubakar.

Alhaji Aminu Atiku ya kuma yi aiki a matsayin Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Zurmi, rawar da jami’an gwamnati suka ce ta ba shi gogewa kai tsaye a harkokin mulki.

Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna kuma ya roƙe shi da ya riƙe gadon magabatansa ta hanyar samar da shugabanci mai dogaro da zaman lafiya, adalci, haɗin kai da walwalar mutanen Zurmi.

A cikin sanarwar da babban mataimakin na musamman kan Kafafen yaɗa labarai a ofishin sakataren gwamnatin jihar, Suleman Ahmad Tudu ya sanya wa hannu, Gwamnan ya bayyana masarautar Zurmi a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin tarihi na Zamfara.

Ya ce masarautar tana taka muhimmiyar rawa a tarihin jihar, wacce ta samo asali daga ilimi, adalci da kuma yi wa mutane hidima.

Gwamnan ya kuma buƙaci sabon sarkin da ya inganta haɗin kai da kuma zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban a cikin masarautar.

Ya kuma roƙe shi da ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro don ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a yankin, wanda ke fuskatar ƙalubalen tsaro a ‘yan shekarun nan.

“Gwamna Lawal ya tabbatar wa sabon Sarkin da goyon bayansa kuma ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa mulkinsa zai bayar da gudummawa mai ma’ana ga zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Masarautar Zurmi da Jihar Zamfara baki ɗaya,” in ji sanarwar.

By ukarofi

Leave a Reply