Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ziyarar ban girma da ya kai fadar Mallamawan Katsina, Hakimin Ɓatagarawa, a ci gaba da rangadin da yake yi a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.
Da yake magana da masu riƙe da sarautun gargajiya a ƙaramar hukumar ta Ɓatagarawa, Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana sarakunan gargajiya a matsayin ginshiƙan zaman lafiya da shugabanci a al’umma.
“Sarakunanmu ginshiƙai ne na zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’ummominmu. Za mu ci gaba da tallafa musu da kayan aiki da muhimman abubuwan da suke buƙata domin gudanar da aikinsu,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa dukkan buƙatun da suka gabatar za a yi la’akari da su gwargwadon abin da ake da shi, yana mai jaddada cewa “Ɓatagarawa na da matsayi na musamman a gare ni,”Inji Dikko.
Ya ƙara da cewa kuɗaɗen gyaran fadar sarakunan gargajiya sun samu gurbi a kasafin kuɗi na ƙananan hukumomi na shekarar 2026, tare da tabbatar da cewa aiwatarwa za ta fara nan da nan.
Gwamna Raɗɗa ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta duba buƙatar ƙarin gina hanyoyi da hakimin Ajiwa, Alhaji Bello Kabir Usman Nogogo ya gabatar, yana mai cewa hanyoyi na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasar tattalin arziki da haɗa kan al’umma.
Da yake magana a madadin hakiman Ajiwa da Ɓatagarawa, Barden Katsina kuma hakimin Ajiwa, Alhaji Bello Kabir Usman, ya roƙi sake gina muhimman hanyoyi da dama, ciki har da hanyar Abukur zuwa Babban Gari,Kawo,Tashar Icce,Bakiyawa, Magamar Ajiwa,Makurda, Babbar RugazuwaJino — dukkaninsu a Ɓatagarawa.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya kuma ƙaddamar da tallafi da shugaban ƙaramar hukumar Ɓatagarawa Babangida Lawal ya samar wa al’ummar yankin.
Sun haɗa da motocin haya 12 da babura 30 domin sauƙaƙa sufuri, injinan ɗinki 100, injinan tace hatsi 100, da injinan nika 100 domin ƙarfafa ƙananan sana’o’i.
Masu cin gajiyar sun kuma samu injinan yin takun spaghetti 50, buhunan fulawa 50, kurajen kwai 300, katon na Indomie 500, buhunan sukari 100, kwalayen madara 100, awaki 100 domin kiwo, da kuma kunshin tallafi na musamman 100 na masu buƙata na musamman.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana tallafin a matsayin shiri na ƙarfafa masu sana’antar cikin gida, tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa, da kuma samar da sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga a cikin ƙaramar hukumar.
Ya ce wannan shiri ya zo daidai da kammala wasu hanyoyin cikin gari a Magamar Ajiwa da kuma kokarin farfaɗo da aikin madatsar ruwa da a da akai watsi da aikin.
Gwamna Raɗɗa ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka da Hon. Babangida Lawal ya kammala, yana mai bayyana su a matsayin ayyukan da suka tabbatar da sadaukarwar gwamnatinsa wajen ci gaban al’umma.
Da yake jawabi gaban dandazon al’ummar yankin, gwamnan ya ce rangadin da yake yi a faɗin jihar na nufin jin buƙatun al’umma kai tsaye, tare da tabbatar masu cewa kokensu da buƙatun za su taimaka wajen tsara ayyukan gwamnati a watanni masu zuwa.
