
Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwmnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya bayar da umarnin a rufe dukkanin makarantun koyon aikin kiwon lafiya masu zaman kansu da ke jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma soke lasisin makarantun bayan wani bincike da ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar ta gudanar game da yadda makarantun ke tafiyar da ayyukansu.
Mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya, Umar Mammada ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu ta Katsina, a ranar Litinin.
Ya ce, a ƴan shekarun nan jihar ta samu ƙaruwar cibiyoyi masu zaman kansu na koyar da kiwon lafiya waɗanda da yawansu ba su da rijista da inganci.
“Yayin da muka amince da muhimmiyar rawar da makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu ke takawa game da yanayin lafiyarmu, yana da muhimmanci a tabbatar da mafi inganci da aminci ga dukkan ƴan ƙasa.”
Ya ƙara da cewa, “Bincike na baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta gwamnatin jihar ta gudanar ya haifar da fargaba kan yadda ake gudanar da ayyukan cibiyoyin horar da kiwon lafiya masu zaman kansu da dama a jiharmu”, inji Mammada.
“Wasu daga cikin waɗannan cibiyoyi ba su cika ƙa’idojin doka da ake buƙata ba don yin aiki a matsayin cibiyoyin horar da kiwon lafiya masu zaman kansu wanda hakan ke haifar da babban haɗari ga jama’a.
“Wannan mataki zai cigaba da aiki har sai an sake yin cikakken nazari tare da gudanar da sabon tsarin rajista, tare da tabbatar da cewa kowacce cibiya ta cika ka’idojin kiwon lafiya da ake buƙata don yin aiki.” Shi.
Daga ƙarshe, gwamnatin jihar ta buƙaci masu tafiyar da makarantun horar da aikin kiwon lafiya a jihar da su gabatar da kansu gaban wani kwamiti na ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar, tare da duk wasu takardu daga ranar 24 zuwa ga watan Satumba, 2024 domin tantancewa da kuma sabunta rijista.
