Zamfara: Magoya bayan Hon. Kabiru Classic sun saya masa takardar takarar shugaban ƙaramar hukuma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Magoya bayan Kabiru Yahaya Classic, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne daga Jihar Zamfara, sun haɗa hannu wajen saya masa takardar tsaya wa takarar kujerar shugaban ƙaramar hukumar Talata Mafara.

Rahotonni sun bayyana cewa, a makon da ya gabata ne aka gudanar da wani taron gaggawa a gidan tsohon ɗan majalisar tsakanin jagorori da magoya bayansa daga mazaɓu 11 na ƙaramar hukumar, wanda ya samu halartar mutane da dama.

An shirya taron ne don tattauna muhimman batutuwa da suka shafi jami’yyar PDP a Talata Mafara musamman saboda yadda Hon. Classic ya nuna damuwa kan Gwamna Dauda Lawal. Ya zargi gwamnan ne da mayar da magoya bayansa masu biyayya saniyar ware duk da sun taka rawar gani yayin nasarar da ya samu a zaɓen 2023.

Classic ya aika da saƙon gargaɗi ga gwamnan, inda ya ba shi mako guda don ya sauya akalarsa, ya na mai cewa amsawarsa ce za ta bayar da alƙibilar siyasarsa.

Wani daga cikin makusantan tsohon ɗan majalisar, mai suna Mu’azu Aliyu ya bayyana irin ɗauki ba daɗin da suka yi da shi inda har rantsuwa ya yi kan cewa ba zai tsaya takarar shugaban ƙaramar hukumar ba, amma duk da haka sai da suka haɗa kuɗi suka saya masa fom ɗin ganin yadda ya ke da tarin magoya baya a yankin nasu.

Kawo yanzu dai ana jiran amsa daga bakin Kabiru Classic kan ƙin karɓa ko amsa buƙatar magoya bayan nasa na shiga sahun ƴan takarar.

Idan za a tuna, Kabiru Classic ne kaɗai ɗan majalisar da ya ƙi bin tsohon gwamnan jihar ta Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, zuwa Jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2023, inda ya zauna shi kaɗai a PDP ya ci gaba da rainonta kuma ya bai wa Gwamna Dauda tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a 2023 lokacin da ya lashe zaɓen.

Wannan ya sa da yawa ke kallon abin da ke faruwa a siyasar PDP a matsayin butulci.

By Babaji