Gwamna Raɗɗa ya shaida haɗarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya shaida munanan haɗuran mota biyu yayin da yake dawowa daga zagayen farko na ziyarar aiki a yankin Funtua.

Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan ya kammala tarurruka a ƙaramar hukumar Matazu.

Haɗarin farko ya faru ne a cikin garin Matazu, inda ayarin gwamnan ya tarar da wata motar Golf ta kasuwanci da ta yi mummunan haɗari. Motar, wadda ke ɗauke da fasinjoji da dama, mutane huɗu sun rasa rayukansu, yayin da mutane goma suka sami raunuka daban-daban.

Gwamna Raɗɗa ya hanzarta bada umarnin a tsaya, ya kuma jagoranci aikin ceto da kansa. Tawagar likitoci da ke cikin ayarin nasa sun bayar da agajin gaggawa yayin jiran ƙarin jami’an lafiya.

Da yake magana a wurin haɗarin, Gwamnan ya ce:
“Babu wani shugaba da ya kamata ya wuce irin wannan ibtila’i ba tare da tsaya ba. Mun tsaya ne domin waɗannan mutanen ’yan’uwa ne. Rayukansu na da muhimmanci, kuma wajibi ne mu nuna tausayi da gaggawa.”

Ya ƙara da cewa:
“Wannan babban rashi tunatarwa ce cewa rayuwa abu ne mai matuƙar rauni. Zuciyata na tare da iyalan waɗanda suka rasu, kuma za mu ci gaba da tallafawa waɗanda abin ya shafa.”

Yayin da Gwamnan ke ci gaba da dawowa Katsina, ayarinsa ta sake cin karo da wani haɗari a kan hanyar Kafinsoli–Koda.

A nan ma gwamnan ya umarci a tsaya. An hanzarta gudanar da aikin ceto, kuma an tura motoci biyu daga ayarin Gwamnan domin kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Charanchi don samun kulawar gaggawa.

Haka kuma Gwamnan yayi jaje ga mataimakin gwamna, wanda shima yaron sa suka yi haɗari akan hanyar Kaduna zuwa Zaria, inda mutane shida suka jikkata.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana baƙin cikinsa kan waɗannan abubuwa, yana addu’a cewa:
“Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta wa waɗanda suka riga mu gidan gaskiya, Ya ba su Aljannatul Firdausi. Ya kuma ba masu jikkata lafiya, Ya mayar da su cikin iyalansu lafiya.”

Gwamnan ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ƙarfafa matakan kariya da tallafi domin kare rayuka da bayar da taimakon gaggawa a lokacin da ake buƙata.

By ukarofi