
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An sake kai wani mummunan hari a Jihar Kano yayin da ƴan bindiga suka kutsa Ƙauyen Ƴan-Kamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa, inda suka halaka wata tsohuwa ƴar shekara 60 da yin awon-gaba da wasu da dama.
Lamarin ya nuna yadda ayyukan garkuwa da mutane ke cigaba da ta’azzara a yankin Arewa ta Yamma.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar yayin da ƴan ƙauyen ke ƙoƙarin koma wa gidajensu, lamarin da ake zargin na faruwa ne sakamakon sulhu da ƴan bindiga mai cike da sarƙaƙiya a yankunan da ke maƙotaka da su.
A cewar shaidun gani da ido, ƴan bindigar sun shiga yankin ne akan babura, inda suka faka su a wani waje gabanin shiga ƙauyen, kana daga bisani suka ƙarasa a ƙafa.
Daga lokacin ne suka ta yin harbe-harbe na kan-mai-uwa da wabi, inda a lokacin ne suka halaka tsohuwar. Sun kuma yi garkuwa da mutane uku yayin da wasu suka tsere zuwa bayan gari.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin a wata sanarwa, inda ya ce tuni aka baza jami’ai domin farauto masu laifin da ƙoƙarin ceto waɗanda aka ɗiba.
