Gwamna Uba Sani na bayar da kyakkyawar kulawa ga inganta lafiyar mata – Hon. Ahmad Yakawada

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

An bayyana Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da cewa yana bai wa harkar kulawa da lafiyar mata da ƙananan yara muhimmanci.

Shugaban ƙaramar hukumar Giwa.Hon.Ahmad Isma’ila Abdullahi Yakawada ne ya bayyanawa yan jarida hakan da yake zantawa da su a tsaka da taron sanin makamar aiki da shugabannin ƙananan hukumomin jihar kaduna 23 a ke gudanarwa a jihar Kano na kwanaki biyar akan abinda ya shafi harkar lafiya da  yadda za su tafiyar da ayyuka domin sauke nauyin al’umma.

Ya ce wannan na ƙara tabbatar da tsarinda Gwamna Uba Sani  ya fito dashi na tallafawa  mata da ƙananan yara a harkar lafiya a faɗin jihar Kaduna.

Ya ce inganta harkar lafiya na daga muhimman ayyuka da gwamna ya sa a gaba tayin tsayin daka akai na tafiyar da dukkan wasu hukumomi don bayar da gudummuwa wajen kula da lafiyar mata da ƙananan yara.

Ya ce dama haƙƙin kula da lafiya na mata da ƙananan yara a matakin farko yana ƙarƙashin ƙananan hukumomi don tafiyar dasu wannan na daga dalilin da ta sa Gwamnan jihar Kaduna ya sahale suka zo suna taron sanin makamar aiki da ake da tunaninsa da goyon baya da jajircewarsa.

Shugaban ƙaramar hukumar Giwa Ahmad Isma’il Abdullahi yace Gwamna Uba Sani ya nuna abinda ya sa a gaba inganta harkar lafiya fiye da komai, yana iya ƙoƙarinsa akai da ake kuma samun gamsuwa akai.

Shugaban na Giwa  Hon. Ahmad Yakawada ya ce zuwansa shugabancin ƙaramar hukumar Giwa sun taradda matsaloli iri-iri dama kuma in ka zo shugabanci matsaloli kake fara nema don ka yi maganinsu, suna kan ƙoƙarin maganinsu, yanzu haka ma sun warware kusan kashi 70 daga ciki, suna sa ran ganin bayan sauran nan bada jimawa ba da yardar Allah.

Ya yi kira ga al’ummar Giwa su cigaba da bayar da goyon baya da yin haƙuri  wani abin sai anyi haƙuri domin wani sai anyi za a ga  amfaninsa, amma lokacin da ake sai a ga kamar ba shi da amfani, suna neman goyon baya da haɗin kan al’umma da gudummuwa na addu’oi da haƙuri  in Alah ya yarda za suyi nasara akan abubuwa da aka sa a gaba.

By ukarofi