Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya bukaci gwamnatin Nijeriya ta gaggauta gudanar da bincike kan iƙirarin da wani dan majalisar dokokin Amurka ya yi na cewa hukumar USAID da gwamnatin Trump ta rufe ta tallafawa ƙungiyoyin ta’addanci da suka haɗa har da Boko Haram a ƙasar.
Ndume ya ce ba batu ba ne da ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗe hannunta, la’akari da girman ɓarnar Boko Haram a jihar Borno.
Ya ce zai gabatar da ƙudiri kan binciken zargin ɗan majalisar dokokin na Amurka.
“In an tashi binciken za mu yi tambayoyi, saboda haka zamu bincika domin mu ‘yan Nijeriya da abun ya shafa ya kamata mu sa ido don a san matakan da za a dauka, saboda ba ƙaramin barna Boko Haram suka yi mana ba,” inji Ndume.
Sanata Ndume ya yi zargin cewa USAID ba ta aiki tare da hukumomin da ya kamata ta yi aiki tare da su a Nijeriya, lamarin da ya ke dasa ayar tambaya, “ba sa bari jami’an tsaronmu su snaya ido kan abubuwan da suke yi ballantana su bada shawara.
Hukumar bada agaji ta Amurka, USAID an ƙirƙire ta a shekarun 1960 domin taimaka wa ayyukan agaji a madadin gwamnatin Amurka a kowanne yanki na duniya.
Tana da ma’aikata dubu 10, wanda kashi biyu bisa uku na aiki a ƙetare. Tana da cibiyoyi a sama da ƙasashe 60, sannan tana ayyuka daban-daban a sauran ƙasashe.
Sai dai galibin ayyukanta wasu ƙungiyoyin take bai wa kuɗi su aiwatar, nata shi ne sa ido da tabbatar da cewa an kashe kuɗaɗen bisa tsari.
Ayyukanta na da ɗimbin yawa. Misali, USAID ba tallafin abinci kaɗai take bayarwa a ƙasashe masu fama da yunwa ba, tana kuma aiki wajen gane inda za a fuskanci fari, da kuma inda za a buƙaci agajin gaggawa na yiwuwar ƙarancin abinci a nan gaba.
Galibin kasafin kuɗin USAID ana kashe su ne a fannin lafiya, irin su rigakafin Polio a ƙasashen da cutar ke yaɗuwa da kuma taimakawa wajen daƙile yaɗuwar cututtuka da ake yi wa kallon annoba.
Sakamakon dakatar da ayyukan na USAID gwamnatin Nijeriya ta ce tana duba yiwuwar fara aiki da mutum 28,000, waɗanda a baya ke aiki da hukumar ba da agaji ta Amurka United States Agency for International Deɓelopment (USAID).
Da yake magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Tɓ ranar Juma’a, ministan lafiya na Nijeriya, Ali Pate, ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar gyara ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar yayin da Amurkar ke janye tallafin da take bayarwa ta hannun USAID.
Ministan ya ƙara da cewa Nijeriya ba ta zuba kuɗaɗe masu yawa ba a ɓangaren lafiyar, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu “a shirye yake wajen sauya alƙiblar tsarin”.
Ya ƙara da cewa fiye da kashi 70 na magungunan da ake amfani da su a Najeirya daga waje ake shiga da su ƙasar.
