Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An ɗage taron Kwamitin Raba Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) da aka shirya yi a ranar Laraba, sakamakon taƙaddamar da ta kunno kai tsakanin Jihohi da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) kan kuɗaɗen da ba a biya ba.
An tattaro cewa gwamnonin jihohin sun ƙaurace wa taron har sai NNPC ya daidaita kuɗaɗen shiga da aka kiyasta kimanin Naira tiriliyan 1.7, wanda ake jira tun bayan cire tallafin man fetur a watan Nuwamba 2024.
Har yanzu dai babu tabbas ko taron zai gudana nan gaba a cikin wannan makon.
Hakan na zuwa ne ‘yan watanni bayan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na fadar shugaban aasa cewa, gwamnatin tarayya ba ta dogara ga kamfanin NNPC wajen biyan buƙatun ta na kuɗi.
Wani babban jami’in hukumar ta NNPC, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, kamfanin na da alaƙa da wasu wajibai, kamar musayar ɗanyen mai da kuma ci gaba da yake amfani da su wajen gudanar da ayyuka. Kuma a cewar jami’in, hakan na shafar kuɗaɗensa.
