Gwamnan Bauchi ya fice daga PDP zuwa APM

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APM, tare da wasu mambobin jam’iyyar da ke goyon bayan shugabancin Tanimu Turaki. Ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati da ke Bauchi a ranar Asabar, inda shugaban APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, ya halarta.

Gwamnan ya ce bayan tattaunawa mai zurfi da shawarwari, sun yanke shawarar shiga APM domin samun nasara a zaɓukan da ke tafe da kuma ci gaba da yi wa jama’a hidima yadda ya kamata. Ya ƙara da cewa dole ne su samar da sahihin dandali na siyasa da zai bai wa magoya bayansu damar tsayawa takara da kuma kare muradun al’umma.

Ya kuma gode wa PDP, wadda ya yi takara a ƙarƙashin ta a shekarar 2019, bisa gudunmawar da ta bayar a tafiyarsa ta siyasa. Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake shirin zaɓukan 2027, inda Bala Mohammed ya ce lokaci ya yi da za su samar da sabon alƙibla da shugabanci ga al’ummar jihar.

By ukarofi