Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sojojin 17 brigade da ke zaune a Katsina sun sami nasarar kashe manyan shugabannin ‘yan bindiga su huɗu tare da gano makamai a hanyar Turare zuwa Yantumaki a ƙaramar hukumar Ɗanmusa.
Majiya daga rundunar sojojin a Katsina sun bayyana ‘yan bindiga suka aikawa sojojin da ke sintiri a hanyar inda sojojin suka sami nasarar kashe mutane huɗu ba tare da wani soja ya sami rauni ba.
Cikin ‘yan bindigan da suka ba kunci lahira akwai Bishir Holami,Jamilu baki, Ibrahim Doro da Abdulrahaman Maje waɗanda hukumomin tsaro suka dangantasu da mummunar hare haren da ake kaiwa al’ummar garuruwan Gobirawa, Raɗɗawa da kiki a ƙananan hukumomin Dutsinma da Matazu.
Hallaka waɗannan manyan yan bindiga ba ƙaramin koma baya ne ga ƙasurgumin ɗan bindiga Muhammadu Fulani wanda ya addabi al’ummar ƙananan hukumomin Musawa, Matazu, Charanchi da kankiya.
Sojojin sun gano bindiga AK 47 harsasshai da kuma Baburan hawa sai kuɗi Naira 153.400 da Wayoyin hannu masu yawa wanda waɗansu na dauke da hotunan yan bindigan sanye da Kayan soja da ake zargi suna amfani da kayan wajan aikata sojan gona.
