Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan Chana a matsayin mashawarci kan tattalin arziki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya naɗa wani ɗan ƙasar China Li Zhensheng a matsayin mai bai wa gwamnatin jihar shawara kan harkokin tattalin arziki.

Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin da yake rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da cibiyar binciken haɗin gwiwa ta duniya ta ƙasar Chana a Bauchi.

Matakin, a cewar gwamnan yana da nufin sanya jihar Bauchi a matsayin wata cibiya ta haɗin gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa, tare da yin haɗin gwiwa na dogon lokaci da ake sa ran za ta ƙara haɓaka zuba jari, da samar da ababen more rayuwa, da haɗin gwiwar bangarorin biyu a fannonin da suka haɗa da noma, ilimi, kiwon lafiya, masana’antu, haƙar ma’adinai, man fetur da iskar gas, da inganta harkokin kasuwanci.

“A wani ɓangare na yarjejeniyar, za a kafa ofishin wakilai na jihar Bauchi a aasar Chana domin sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan da kuma tabbatar da isar da sahihancin lokaci,” inji shi.

Yarjejeniyar ta zayyana tsarin haɗin gwiwa, tare da takamaiman yarjejeniyoyin ayyuka da za a haɓaka bisa ga kowane hali.

Gwamnan ya bayyana cewa, ƙawancen ya yi daidai da tsarin diflomasiyya tsakanin shugaba ɗi Jinping na ƙasar Chana da Bola Tinubu na Nujeriya, wanda aka tsara don ƙarfafa dangantaka a matakin ƙasa baki ɗaya.

“Wannan yarjejeniya ba ta shafi ababen more rayuwa ba ne kawai, tana nufin gyara rayuwa ne, muna buze Bauchi ga duniya,” inji shi, ya aara da cewa haɗin gwiwar za ta bunƙasa zuba jari kai tsaye daga ƙasashen waje, da samar da ayyukan yi, da inganta sana’o’i, da sabunta muhimman sassa, da inganta yanayin Bauchi a duniya.

A nasa jawabin, Zhensheng, wanda shi ne shugaban cibiyar bincike ta haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa ta aasar Chana, ya yi alƙawarin ci gaba da haɗa albarkatun ƙasa da ƙasa don tallafawa ci gaban tattalin arzikin Bauchi.

“Mun himmatu wajen taimaka wa Bauchi wajen samun ci gaba mai ɗorewa, samar da ababen more rayuwa na zamani, da inganta rayuwa,” inji shi.

By ukarofi