Ranar Jinƙai ta Duniya: ’Yan Nijeriya miliyan 31 na fuskantar yunwa – Majalisar Ɗinkin Duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar ɗinkin Duniya ta fitar da wani sabon rahoto game da taɓarɓarewar al’amuran jinƙai a Najeriya, inda ta yi gargaɗin cewa ‘yan Nijeriya miliyan 31 ne ke fama da ƙarancin abinci, yayin da sama da yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar miliyan 10 ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, ciki har da miliyan 3.5 da ke fama da matsananciyar yunwa.

An bayyana wannan mummunar ƙididdigar ne a wani taron haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar ɗinkin Duniya (UNOCHA) suka gudanar a Abuja ranar Talata, domin bikin ranar jinƙai ta duniya na shekarar 2025, mai taken “ƙarfafa Haɗin Kan Duniya da ƙarfafa Haɗin kan ƙananan ƙaukayu.”

Da yake jawabi a wurin taron, babban jami’in kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Cinkin Duniya a Nijeriya, Mohamed Fall, ya yi gargaɗin cewa buƙatun jinƙai a Nijeriya na ta’azzara cikin wani yanayi mai ban tsoro, inda matsalar ƙarancin abinci da rashin abinci mai gina jiki na aananan yara ke kai wani matsayi.

“A halin yanzu, an kiyasta cewa mutane miliyan 31 ne ke fama da ƙarancin abinci, sama da yara miliyan 10 ‘yan ƙasa da 5 suna fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, kuma miliyan 3.5 na fuskantar matsananciyar rashin abinci mai gina jiki,” inji Fall.

Ya koka da cewa, bikin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun koma baya ga haɗin kan duniya ga mutanen da ke buƙata, tare da rashin kula da kuɗaɗen jinƙai na ƙasa da aasa da kuma rashin kula da dokokin jinaai.

Ya ƙara da cewa, “Al’ummar masu buƙatar ayyukan jinƙai na fuskantar ƙalubalen da ba a taɓa ganin irinsa ba, tare da samun ƙaruwar yunwa a duniya,” inji shi.

Fall ya yi kira da a yi sauye-sauye cikin gaggawa a cikin tsarin jinƙai, yana mai jaddada buƙatar ƙarfafawa ‘yan gida da kuma tabbatar da martanin jinƙai da gwamnati ke jagoranta, al’umma ne ke tafiyar da su, kuma masu ɗorewa.

Ya buƙaci a sauya tsarin dogaro da kai ga tallafin da ƙasashen duniya ke bayarwa zuwa shirye-shiryen cikin gida, yana mai cewa:

“Ya zuwa ƙarshen lokacin miƙa mulki, ya kamata ƙasashen duniya su mayar da hankali wajen ba da dama ga ‘yan cikin gida maimakon kai agajin waje.”

ƙaramin Ministan Harkokin Agaji da Rage Talauci na Nijeriya, Dr. Tanko Sununu, ya jaddada ƙudirin gwamnati na ƙarfafa tsarin jinƙai ta hanyar ƙara kuɗaɗe da tabbatar da bin diddigi.

“Gwamnatin Nijeriya ta fahimci muhimmancin danganta taimakon jin ƙai da ayyukan ci gaba da zaman lafiya,” inji Sununu.

“Saboda haka, gwamnati na shirin ƙara kuɗaɗe don ayyukan jin ƙai da kuma kafa tsarin tabbatar da gaskiya.”

Gwamnatin Nijeriya da Majalisar ɗinkin Duniya sun yaba wa ma’aikatan jinƙai musamman ma’aikatan ƙasar, waɗanda suka rasa rayukansu yayin da suke kai agaji ga waɗanda rikici da bala’o’i ya shafa.

Fall ya jaddada cewa dole ne ayyukan jinƙai a Nujeriya su kasance masu inganci, gaskiya da riƙon amana, yayin da Sununu ya jaddada ƙudirin gwamnati na haɗa hannu da ƙungiyoyin aasa da ƙasa don rage raɗaɗin talauci.

By ukarofi