Gwamnan Filato ya fice daga PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance, lamarin da ya kawo ƙarshen dogon zangon da ya yi acikinta da kuma nuna sabuwar alƙiblar siyasa a jihar.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Disamba, 2025, wanda ya aike wa Shugaban jam’iyyar na Gundumarsa ta Ampang ta Yamma a Ƙaramar Hukumar Mangu, wato Dasjak Sunday Longyol.

Saidai, Gwamna Mutfwang bai bayyana cikakken dalilinsa na ficewar ba, amma ya nuna cewa hakan ya yi daidai da burinsa na cigaba da yi wa al’ummar jihar hidima.

Ya kuma yi wa jam’iyyar godiya bisa yadda ta ba shi dama shiga sahun waɗanda suke yi wa al’umma hidima a ƙarƙashin dimukraɗiyyar da kuma goyon bayan da ya samu daga jagororin jam’iyyar, mambobi da magoya bayanta.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da samun sauye-sauyen sheƙar, manyan ƴan siyasa musamman gwamnoni daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a fadin ƙasar.

Zuwa yanzu dai babu tabbacin jam’iyyar da Gwamna Mutfwang zai koma, ko kuma matakin da PDP za ta ɗauka dangane da matakin nasa.

By ukarofi