Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Aƙalla manoma 75,000 daga ƙananan hukumomi 16 na Jihar Kano ake sa ran za su amfana da shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki ta hanyar noma a ƙarƙashin shirin Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ), wani babban shirin gwamnatin tarayya da ke samun tallafi daga Bankin Raya Afirka (AfDB), IFAD, Bankin Raya Musulunci, da sauran abokan hulɗa na ci gaba.
An bayyana hakan ne a ranar Laraba a Kano wanda ƙwararre a harkar sadarwa na shirin, Malam Shehu Babangida, yayi a wani taron horaswa na kwana guda ga kafafen yaɗa labarai kan Sauya halayen al’umma (BCC) domin inganta abinci mai gina jiki, wanda aka shirya domin manoma, ‘yan jarida da ma’aikatan lafiya.
Babangida ya bayyana cewa shirin SAPZ an tsara shi ne domin haɓaka yawan amfanin gona tare da magance matsalolin rashin ingantaccen abinci, ta hanyar inganta dabarun noma, ƙarfafa sarkar darajar amfanin gona, da wayar da kan al’umma kan cin abinci mai gina jiki.
A cewarsa, an riga an tattara bayanai na kimanin manoma 16,000 daga ƙananan hukumomi takwas, yayin da ake sa ran ƙarin manoma 9,000 na noman rani za su amfana da ɓangaren shirin da ya shafi gina jiki.
Da take nata jawabin, Hajiya Rabi Mustafa Sadiq, jami’ar sadarwa ta shirin SAPZ Kano, ta ce shirin ya mayar da hankali kan farfaɗo da noman tumatir, sesame, gyada da shinkafa, tare da inganta sarrafa amfanin gona da samun kasuwanni.
Ta ƙara da cewa ana aiwatar da shirin ne a matakai, inda mataki na farko ya shafi ƙananan hukumomi 16 na jihar Kano, tana mai cewa wannan tsari zai taimaka wajen sake fasalta harkar noma a matsayin ginshiƙin tattalin arziki mai tushe a gina jiki.
Shi ma da yake na sa bayanin Dr. Auwalu Musa Umar, babban jami’in gina jiki a ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano, ya ce gwamnatin jihar ta umarci hukumar kididdiga da ta samar da sabbin bayanai kan manoma domin inganta tsare-tsare da aiwatar da shirye-shirye masu tasiri a fannonin noma da gina jiki.
A nasa jawabin, Dr. Bashir Sunusi, babban sakatare a ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa ta Jihar Kano, ya jaddada ƙudurin gwamnatin jihar na haɓaka noma da kiwo domin tabbatar da wadatar abinci.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta zuba jari mai yawa a fannin samar da abinci ta hanyar gyaran dam-damai, farfaɗo da magudanan ruwa domin bunƙasa noman rani, da kuma ɗaukar ma’aikata 1,038 don tabbatar da inganci da nagartar ayyuka.
Taron ya kammala da kira ga ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shirin SAPZ da kafafen yaɗa labarai, domin ci gaba da wayar da kan jama’a kan noma mai la’akari da gina jiki, yayin da shirin ke da burin ƙara yawan kuɗin shigar manoma, samar da ayyukan yi, da ƙarfafa tsaron abinci a Jihar Kano.
