Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanatan da ke wakiltar Jihar Nasarawa ta Arewa a Majalisar Dattawan Nijeriya, wato Godiya Akwashiki, ya rasu a ranar Alhamis a wani asibitin ƙasar Indiya bayan shafe shekaru 52 a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa Sanatan ya yi fama da wani rashin lafiya ne ne ɗan wani lokaci, wanda hakan ya sa aka garzaya da shi Indiya domin neman magani.
A ranar 3 ga watan shekarar 1973 ne aka haifi Akwashiki a garin Angba Igga da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa Eggon ta jihar.
Ya kuma riƙe muƙaman jagoran mafiya rinjaye da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar ta Nasarawa.
Akwashiki ya zama zaɓaɓɓen sanata ne a shekarar 2019 ƙarƙashin jam’iyyar APC, sannan kuma aka sake zaɓar sa bayan koma wa SDP a 2023.
Wani mataimaki ga marigayin mai suna Ajegena Likita Ibrahim ne ya tabbatar wa jaridar Daily Trust rasuwar, inda ya bayyana al’amarin a matsayin “babban rashi”.
Ya kuma shaida wa manema labarai cewa suna tattaunawa da iyalan mamacin da ke Indiya domin ganin an kawo gawarsa gida Nijeriya, inda tuni aka fara shirye-shiryen jana’izarsa.
