Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta jaddada tsattsauran matakan da aka ɗauka na tantance lafiyar maniyyata a yayin aikin Hajjin 2026, inda ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci rashin cika ƙa’idojin kiwon lafiya da ƙasar Saudiyya ta gindaya ba.
Hukumar ta jaddada wannan mataki ne a yayin zaman da ta yi da jami’an tawagar lafiya daga jihohin Nijeriya wanda ta yi a Abuja a ranar Talata.
A yayin zaman, wanda Manhaja ta bibiya, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya ce, lallai ne a cika dukkan ƙa’idojin lafiya da Saudiyya ta shar’anta.
Shugaban ya jaddda cewa ba ɗaga ƙafa wajen cika ƙa’idojin saboda kai tsaye sun shafi ma’aunin gwada nasarar aikin Hajjin 2026 da za a yi.
Ya kuma yi kira da a samu haɗin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki, yana mai cewa kyakkyawan tsarin lafiya muhimmin abu ne wajen samun nasarar aikin hajjin bana.
A yayin taron, an yi kira ga jihohi da su ƙara jaddada batun gwajin lafiya da tabbatar da ma’aikatan lafiya sun yi aiki yadda ya kamata a yayin gwajin lafiyar.
Sannan hukumar ta sake duba wasu daga cikin cutattukan da Saudiyya ta ce ba ta lamunta su je aikin hajji ba a bana.
Waɗannan cutattuka sun haɗa da gazawar wasu sassa na jiki da cuta mai tsanani da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa da cututtuka masu yaɗuwa da masu fama da kansa da ke shan magani da mata masu juna biyu.
Sannan wajibi ne a yi allurar rigakafin Kwabid-19 da cutar shawara (yellow fever) da sauransu.
Shugaban ƙungiyar sakatarorin hukumar l alhazan jihohi, Idris Almakura, ya bayyana cewa tawagar likitoci ta qasa ginshiƙi ne na samun nasarar aikin Hajji.
Ya buƙaci likitocin da su nuna ƙwarewa da gaskiya da aiki tuƙuru a yayin gwajin lafiyar, yana mai gargaɗin cewa aikinsu kai tsaye abu ne da zai shafi lafiya da rayuwar maniyyata.
Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin fara shiri da wuri da kafa cibiyoyin lafiya da jan hankali kan kauce wa jan qafa da aka samu a yayin shirin aikin Hajjin da bara.
Manhaja ta rawaito cewa NAHCON ta riga ta fara ɗaukar ma’aikatan lafiyar aikin Hajjin shekarar 2026.
Hukumar ta ce an ɗau wannan mataki ne domin tabbatar da an ɗauki ƙwararrun likitoci akan lokaci.
NAHCON ta sanar da cewa ƙa’idojin ɗaukar ma’aikatan na bana sun haɗa da sauya waɗanda suka gudanar da aiki a bara.
Kuma an shawarci masu neman aikin a bana da su kula da su sosai a yayin cike takardar neman gurbin da kula da wa’adin lokaci da aka ɗiba don gudun kada su gaza samun shiga cikin waɗanda za a tantance.
A ƙoƙarin magance ƙalubalen lafiya ke jawo tsaiko, mahukunta a qasar Saudiyya don gindaya sharuɗa na ƙarfafa yin gwajin lafiyar alhazai a shekarun bayan nan, inda ta ɗora wa ƙasashe nauyin kula da tabbatar da an gudanar da gwajin lafiya kafin zuwa gudanar da aikin.
Duk da nanata wannan gargaɗi da mahukunta a Nijeriya ke yi, an samu wasu alhazai da suke masu juna biyu da sauran matsaloli na lafiya da ke tsallake matakan gwajin lafiyar.
Wannan matsaloli ne ya sa aka ɗiga alamar tambaya kan sahihancin tsarin gwajin lafiyar inda mahukunta suke ƙara tsaurara matakan a qasa da ma jihohi bakiɗaya.
A yayin aikin Hajjin 2025, mata ‘yan Nijeriya 6 ne aka samu sun yi varin ciki a yayin aikin Hajji a yayin da wata mata daga jihar Zamfara ta haihu a Madina bayan kwanaki da isa domin sauke farali a Saudiyya.
Wannan lamari ya nuna irin haɗarin da rashin gudanar da sahihin gwajin lafiya ke haifarwa wanda ya sa aka tsaurara matakan a bana.
