Kwato dazuka daga hannun ’yan ta’adda

Spread the love

Sanarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi cewa daga yanzu ’yan fashi, masu garkuwa da mutane, ƙungiyoyin daba da duk wasu masu riƙe da makamai za a riƙa ɗaukarsu a matsayin ’yan ta’adda, alama ce ta sabon salo a tsarin tsaron Nijeriya. Wannan matsaya, da aka bayyana yayin gabatar da kasafin kuzin shekarar 2026, ta zo ne tare da shirin tura jami’an tsaron gangun daji sama da 7,000 a jihohi bakwai, wato Borno, Sakkwato, Yobe, Adamawa, Neja, Kwara da Kebbi zuwa cikin dazuka.

Tambayar da ke yawo a zukatan ’yan Nijeriya ita ce: shin wannan sabon tsari zai yi nasara inda tsofaffin dabaru suka gaza?

Mayar da ’yan fashi da masu garkuwa da mutane matsayin ’yan ta’adda ba magana ce ta suna kawai ba. Sauyi ne mai zurfi da ke canja tsarin doka da yadda jami’an tsaro ke tunkarar waɗannan miyagun laifuka.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana hakan ƙarara inda ya ce duk wanda ke addabar al’umma, ko mutum ne ko ƙungiya, to ɗan ta’adda ne, babu wata kafa ta ɓoye sunan laifi. Wannan furuci na nufin rufe giɓin da tsawon lokaci ya bai wa ƙungiyoyin laifi damar yin ɓarna cikin walwala a manyan wuraren da gwamnati ba ta da cikakken iko.

Shirin Jami’an Tsaron Gandun Daji ya nuna fahimtar gaskiyar da masana tsaro ke faɗi tun shekaru da dama: rundunar soja kaɗai ba za ta iya tsare manyan dazukan Nijeriya ba. Waɗannan jami’ai 7,000 da aka horas an ɗauko su ne daga yankunansu, abin da ke ba su cikakken sanin ƙasa, al’umma da dabarun miyagun laifuka, wanda jami’an da ake kawowa daga waje galibi ba su da shi.

Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana su a matsayin jami’an gaggawa da za su mamaye dazuzzuka, su tattara bayanan sirri tare da tallafa wa sauran ayyukan tsaro.

A ɓangaren dabaru, wannan tunani yana da tushe. Dazukan Nijeriya sun zama mafakar ’yan ta’adda ne saboda rashin cikakken ikon gwamnati a cikinsu. Sansanonin ’yan fashi, maɓoyar masu garkuwa da mutane da haramtattun masu haƙar ma’adinai sun yawaita a wuraren da babu tsaro. Tura jami’ai ’yan asalin yankuna da ke da amincewar al’umma na nufin kwace muhimmin makamin da miyagu ke da shi, wato mafaka.

Sai dai ba wannan ne karon farko da Nijeriya ke jin kalaman tsaro masu kaushi ba. Gwamnatoci da dama sun sha ayyana yaƙi da ’yan fashi da ’yan ta’adda, sun kafa sabbin tsare-tsare, amma sakamako ya kasance marar gamsuwa. Me ya bambanta wannan karon?

Akwai abubuwa uku da ke jan hankali. Na farko shi ne mayar da waɗannan miyagun laifuka matsayin ta’addanci, wanda ke ƙara ƙarfin hukunci a kotu. Na biyu shi ne dogaro da ilimin yankuna ta hanyar ɗaukar jami’ai ’yan asalin yankin. Na uku kuma shi ne haɗin gwiwar hukumomi da dama, ciki har da DSS, rundunar soja, ’yan sanda da jami’an NSCDC. Duk da haka, akwai damuwa da ke rage farin ciki.

Adadin jami’ai 7,000 da za a raba a jihohi bakwai masu faɗin dazuka ya haifar da tambaya kan ko wannan yawan zai wadatar wajen tinkarar ƙungiyoyin da suka shafe shekaru suna kafa ƙarfi da makamai. Haka kuma, ɗaukar jami’ai daga yankuna na iya fuskantar matsin lambar alaƙa ta ƙabila ko iyali, da kuma yiwuwar kutsen miyagu. Don haka, dole ne a samar da tsauraran hanyoyin sa ido da canja wurin aiki domin kare tsarin daga lalacewa.

Haɗin gwiwar hukumomi shi ma babban ƙalubale ne. Tarihin tsaron Nijeriya ya nuna rikicin iko, ɓoye bayanai da rarrabuwar aiki tsakanin hukumomi. Samar da umarni ɗaya tilo da aiki cikin haɗin kai, tare da shigar da sabuwar runduna, ba aiki ne mai sauƙi ba.

A ƙarshe, muhimmin abu shi ne sakamako. ’Yan Nijeriya sun gaji da ‘gafara sa ban ga ƙaho ba’, ma’ana jin sabbin tsare-tsare ba tare da ganin canji a rayuwarsu ba. Abin da suke so shi ne su yi tafiya ba tare da tsoron za a iya sace su ba, su noma gonakinsu ba tare da fargabar ’yan fashi ba, su kwanta barci cikin kwanciyar hankali. Shirin Tsaron Dazuka ya cancanci goyon baya da lokaci, amma kuma ya cancanci cikakken bincike da gaskiya a sakamako.

Zamanin ɓoye suna da ruɗani ya kamata ya ƙare. Abin da ya rage shi ne a nuna wa ’yan Nijeriya dazuka masu tsaro, hanyoyi masu aminci da al’umma da aka kare. Wannan ne ma’aunin da zai tabbatar da nasara ko akasin haka.

By ukarofi