Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekara ta 2026 da ta kai naira tiriliyan 1.47, wadda ke kafa tubalin aiwatar da shirye-shiryen ci gaban jihar a shekarar kuɗi mai zuwa.
Gwamnan ya amince da kasafin kuɗin ne a ranar Laraba, yayin wani taron majalisar zartarwa ta Jihar Kano da aka gudanar a Kano.
Dokar kasafin kuɗin, wadda ta kai ₦1,477,829,666,131, majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita a makon da ya gabata, a zaman majalisa da Kakakin Majalisar, Alhaji Ismail Falgore, ya jagoranta.
An zartar da ƙudirin bayan tattaunawa mai zurfi a kwamitin gaba ɗaya (Committee of the Whole), tare da karanta shi karo na uku da magatakardar majalisar, Alhaji Bashir Diso, ya yi, abin da ke nuna yadda majalisar ta yi cikakken duba kan fifikon kashe-kashen kuɗin jihar.
A baya, Gwamna Yusuf ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na naira tiriliyan 1.36 ga majalisar, wanda ya sanya wa suna “kasafin kuɗin ginshikin ababen more rayuwa, haɓaka ci gaban jama’a da ɗorewar ci gaba.” Kasafin na da nufin ci gaba da ayyukan da ake gudanarwa tare da gabatar da sabbin tsare-tsare a muhimman sassa na tattalin arziƙin jihar.
Wakilin Blueprint Manhaja na Kano, ya ruwaito cewa wannan sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin, Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tsaf domin aiwatar da kasafin shekarar 2026 gaba ɗaya, tare da ƙarfafa aniyarta kan bunƙasa ababen more rayuwa, haɓaka tattalin arziƙi mai haɗa kowa, da kuma tafiyar da mulki mai ɗorewa.
