Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bai wa maniyyata shawara kan su tabbata suna cikin ƙoshin lafiya kafin tafiya aikin Hajjin 2025.
Gwamnan ya buƙaci al’umma da su cigaba da gode wa Allah albarkacin watan Ramada da ibadar azumi da aka kammala.
Ya yi wannan kira ne a ranar Talata a yayin bikin sallah da ma’aikatar cikin gida ta jihar ta shirya wa gwamnan.
Taron mai taken, “A shirye nake ya ubangiji da kowanne alkhairi da ka aiko min” kuma an yi taron ne a gidan gwamnatin da ke Marina.
“Nan da watan Mayu masu niyya za su fara tafiya aikin Hajjin bana, don Allah ku tabbata kuna cikin ƙoshin lafiya.
“Idan akwai wata rashin lafiya da ke damunki, ku kaucewa zuwa aikin Hajjin 2025, ku tsaya a nan gida ku yi addu’o’inku.”
Sannan gwamnan ya taya al’ummar musulmi murnar kammala ibadar azumin watan Ramadana.
“Ina addu’ar Allah ya cigaba da zaunar da mu cikin aminci da haɗin kai da ba mu damar ganin sallar baɗin-baɗaɗa.”
“Ina gode wa dukkan malaman addini kan yadda suka ilimantar da mu littafi mai tsarki, ina yi mana fatan gudanar da bikin sallah cikin ƙoshin lafiya.”
A nata jawabin, uwargidan gwamnan jihar Legas, Dr Ibijoke Sanwo-Olu, ta roƙi al’ummar jihar da su cigaba da nuna jinƙai ga marasa ƙarfi.
“A yayin da muke bikin Sallah, akwai buƙatar mu tuna da marasa ƙarfi da ke cikinmu domin mu tallafa musu.
“Bauta ba ta tsaya ga ibada ba, yadda muka mu’amalanci juna na da muhimmanci wajen kyautata jiharmu da ƙasa bakiɗaya.
“Ina roƙonmu da mu cigaba da yin imani da kuma dagewa wajen gudanar da addu’o’i.”
Babban baƙo mai jawabi, Dr Munirudeen Ar-Riyardy, daga jami’ar jihar Legas ya ba wa ‘yan Nijeriya shawarar su kauce wa aikata saɓo domin samun yardar Ubangiji.
“A yau wannan lakca a kan irin ƙaddarar da ke samun mu ne a rayuwa da yadda za mu iganta imaninmu duk kuwa da ƙalubalen da ake fama da su. Bai kamata mu riƙa tsine wa shugabanninmu ba, kuma mu kaucewa aikata saɓo.”
Shi ma mataimakin gwamnan jihar Obafemi Hamzat ya yi kira ga al’ummar jihar Legas da su kyautata wa junansu.
“Ku nuna tausayin juna da kyautatawa ga maƙwabtanku da ƙara yin imani da Allah,” ya faɗa.
Kwamishinan harkokin cikin gida, Ibrahim Layode, ya buƙaci musulmai su cigaba da yin koyi da koyarwar addinin Musulunci.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da: Matar mataimakin gwamnan, Oluremu da mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin addini, Alhaji Abdullah Jebe, da babban ilimin jihar Legas, Shaykh Suliamon Abu-Nolla.
