Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamandan birget ta ɗaya ta sojojin Nijeriya a jihar Zamfara, Birgediya-Janar Timothy Opurum, ya ce dakarunsa ƙarkashin rundunar Fansar Yamma, sun samu nasarar rage ayyukan ‘yan ta’adda a yankin – wanda ya ƙunshi jihohin Kebbi da Zamfara.
Janar Opurum ya bayyana haka ne ranar Talata yayin taron cin abinci don murnar sallah ƙarama da aka shirya wa sojoji da iyalansu a sansanin birget ɗin da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
A cewarsa, a baya lamarin tsaro a yankunan ya zama babban ƙalubale, amma bisa jajircewar dakaru da kuma farmaki akai-akai, an samu gagarumin nasara wajen rage ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.
“Birget ta ɗaya na aiki tuƙuru a ayyukanta a faɗin yankin, musamman na ayyukan rundunar operation forest sanity III. A watannin baya lamarin ba shi da kyau duk da jajircewar dakarunmu, amma yanzu mun samu galaba kan ‘yan bindigar da suka addabi yankin – mun rage barazanarsu kan al’umma,” inji janar Opurum.
Ya yaba wa dakarun bisa sadaukarwar da ya ce suna yi wajen daƙile ayyukan ‘yan bindiga, inda ya ce kan haka ne ma shugaban rundunar sojin ƙasa ya amince da aika ƙarin kayayyakin aiki domin taimaka wa sojojin.
Ya buƙaci sojojin da su jajirce su kuma ƙara himma wajen ganin dukkan jihohi da ke arewa maso yamma sun samu isasshen tsaro da kuma zaman lafiya.
