Gwamnatin Gombe ta haramta sana’ar bola jari saboda tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Inuwa Yahaya ta sanar da zaukar tsauraran matakan tsaro masu faɗi, da nufin ƙarfafa zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

Matakan sun fito ne bayan wani taron Kwamitin Tsaro na Jihar da Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta, domin duba sabbin barazanar tsaro da kuma wasu munanan al’amura da suka faru a baya-bayan nan. Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barrista Zubair Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron.

Barrista Zubair Umar ya ce bayan nazari mai zurfi kan rahotannin lalata kadarorin gwamnati, musamman makarantu da sauran muhimman ababen more rayuwa, Kwamitin Tsaron ya amince da haramta gwangwan, wanda aka fi sani da bola jari, nan take a faɗin jihar.

A cewarsa, an zauki matakin ne saboda rawar da wannan kasuwanci ke takawa wajen tayar da barazana ga tsaro.

Ya bayyana cewa gwamnatin ta lura da yadda ake ci gaba da lalata gine-ginen makarantu da kadarorin jama’a, inda galibin kayan da aka lalata ke ƙarewa a hannun ’yan kasuwar Bola Jari. 

Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan yadda ’yan kasuwar ba su da tsari mai ƙarfi, jagoranci guda, ko tsarin sa-ido na gwamnati, lamarin da ke wahalar da hukumomi wajen sa ido da shawo kan ayyukansu.

Barrista Zubair Umar ya ce haramcin zai ci gaba da aiki har sai ’yan kasuwar sun haɗa kansu ƙarƙashin ingantaccen shugabanci da aka amince da shi, sannan gwamnati ta ware musu wuri na musamman da za su riƙa gudanar da kasuwancinsu ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

Dangane da yanayin tsaro na ƙasa baki ɗaya da tasirinsa ga Jihar Gombe, Babban Lauyan Jihar ya bayyana cewa Kwamitin ya yanke shawarar ƙara tsaurara sa-ido, musamman kan mutanen da ke shigowa jihar domin zama. Ya ce daga yanzu duk wanda ke shigowa Gombe don zama ko hayar gida dole ne a tattara cikakkun bayanansa, domin sauƙaƙa aikin tattara bayanan sirri da kuma bai wa hukumomin tsaro damar bincike idan buƙatar hakan ta taso.

Akan rikicin manoma da makiyaya, Barrista Zubair Umar ya bayyana cewa gwamnati ta kafa wani kwamitin aiwatarwa domin tabbatar da aiwatar da shawarwarin da ke cikin Farar Takarda kan ajiyoyin kiwo da hanyoyin shanu. Farar Takardar ta biyo bayan rahoton wani kwamiti da wani tsohon Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda, AIG Zubairu Muazu (mai ritaya), ya jagoranta, wanda ya yi nazari kan halin da ajiyoyin kiwo da hanyoyin shanu ke ciki a jihar.

Ya ce, aikin kwamitin shi ne tabbatar da kwato duk wata ƙasa ta ajiyoyin kiwo da hanyoyin shanu da aka mamaye ba bisa ƙa’ida ba, domin rage rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummomi.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Gombe, CP Umar Ahmad Chuso, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun ƙara zage damtse bayan wasu hare-hare da suka haɗa da sace-sace da kisan kai a Pindiga, ƙaramar hukumar Akko. Ya bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici, amma ya tabbatar wa al’umma cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace tare da kamo masu laifin.

Haka zalika, Sarkin Yamaltu, Alhaji Abubakar Aliyu, ya ce Kwamitin Tsaron ya yanke shawarar ƙara ƙarfafa tsaro a matakin ƙananan hukumomi ta hanyar amfani da ’yan sa-kai da mafarauta na gargajiya, domin su taimaka wa hukumomin tsaro na zamani wajen sa-ido da kai ɗauki cikin gaggawa.

Gwamnan ya kuma bayar da umarni ga shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya da su riƙa gudanar da tarukan bitar tsaro kowane mako, domin nazarin halin da ake ciki da ɗaukar matakan rigakafi don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Gombe.

By ukarofi