Gwamnatin Jihar Katsina ta janye ƙarar da take wa tsohon gwamnan jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta janye ƙarar da ta shigar gaban kotu, inda take zargin tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shehu Shema da kuma tsohon shugabannin ƙananan hukumomin jihar Ibrahim Lawal Ɗankaba bisa zargin karkatar da Naira biliyan 11 daga asusun ƙananan hukumomin jihar.

Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar shari’a Abdulrahman Umar ya bayyana haka lokacin da yake yi wa manema labarai bayani dangane da lamarin.

Ya bayyana cewar janye ƙarar ya biyo bayan wata takarda da gwamnatin jihar ta aike wa kotun da aka shigar da ƙarar gabanta.

Ya ci gaba da cewa kotu ta amince da buƙatar da gwamnatin ta shigar na janye dukkan ƙarar da ta shafi almundahana da aikata ba daidai ba da ake wa tsohon gwamnan da kuma Lawal Ɗankaba.

Sai dai ya bayyana cewar ban da ƙarar da hukumar EFCC ta shigar a Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Katsina, inda ake zargin gwamnan bisa laifin wawure kuɗin tallafin shirin SURE- P Naira biliyan 5.7

“Mun je kotun da buƙatar janye ƙarar wadda kowane babban mai shari’a a jiha yana da dama da kuma ikon gabatar da kowane mutum gaban kowace kotu a Nijeriya kamar yadda yake da ikon janye kowace shari’a ko ƙara da aka shigar gaban kotu.

“Babbar mai shari’a ta yi amfani da wannan dama kuma kotu ta yi maraba da wannan buƙata da babbar mai shari’a ta jiha ta shigar, don haka an sallami tsohon gwamna da Lawal Ɗankaba daga tuhumar da ake masu.

“Wannan ita ce matsayar gwamnatin jiha zuwa yanzu, sai dai shari’ar tsohon gwamnan da hukumar EFCC tana nan tana ci gaba da wakana,” inji shi.

Ibrahim Shehu Shema ya zama gwamnan jihar Katsina daga 2007 zuwa 2015 sai dai tun bayan da Gwamna Aminu Bello Masari ya karɓi mulkin jihar gwamnatin jihar Katsina ta maka Shema da wasu muƙarrabansa kotu a shekarar 2016 da suka haɗa da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu Alhaji Sani Hamisu Makana, babban sakatare a ma’aikatar Alhaji Lawal Rufa’i da kuma shugabannin ƙananan hukumomin jihar Lawal Ɗankaba bisa zargin aikata laifuffuka da suka haɗa da cin amana, zamba, almundahana da karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar waɗanda suka kai Naira biliyan 11.

Sai dai tsohon gwamnan jihar a Jam’iyyar PDP ya musanta dukkan laifukan da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari ke tuhumarsa.