Ƙarancin Naira da man fetur barazana ce ga takarar Tinubu – Gbajabiamila

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya danganta matsalar da ake fuskanta a halin yanzu na ƙarancin man fetur da ƙarancin Naira ka iya daƙile nasarar ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu na cin zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne a Legas ranar Talata a lokacin ƙaddamar da shirin raba motocin sufuri mai taken: ‘Gbaja Ride’ ga mazaɓarsa ta Surulere.

Motocin bas guda 35 masu saukin farashi za su riƙa bin hanyoyi daban-daban a Surulere da kewaye.

“A matsayina na wakilinku kuma mai magana da yawunku, Ina da kyakkyawar fahimta game da wahalhalu da rashin jin daɗin da ‘yan Nijeriya da dama ke fuskanta, ba tare da bambanta da ‘yan mazaɓa na ba,” inji Gbajabiamila.

“Majalisar dokokin da ke ƙarƙashin jagorancina ta kasance a ɓangaren jama’a, suna aiki tuƙuru domin kuɓutar da su daga waɗannan matsaloli.

Na ji daɗin yadda ma’aikatar shari’a ta tabbatar da matsayarmu kan aiwatar da manufar sake fasalin Naira.”

Ya bayyana cewa sabuwar manufar kuɗin Naira wani shiri ne da aka yi tunani sosai, wanda kuma abin takaici an yi garkuwa da shi, aka kuma sanya shi a siyasance, inda ya yi zargin cewa wasu abubuwa ne suka haifar da rikicin da ke tattare da manufar hana Tinubu zama Shugaban Ƙasa na gaba.

Gbajabiamila ya ce da alama wannan makircin ya ci tura domin har yanzu ‘yan Nijeriya sun ci gaba da riƙe amana da Jam’iyyar APC da Tinubu duk da ruɗanin da ya biyo bayan larancin Naira.

“Ba wanda zai iya gamsar da ni cewa ba makirci ba ne na hana Asiwaju zama Shugaban ƙasar nan ba. Amma na yi farin ciki da cewa Ubangijinmu yayin da mutanen nan suka zauna tare don ƙulla makirci ya shiga tsakani,” inji Gbajabiamila.