Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da gudanar da babban bikin gargajiya na masarautar Bichi mako guda kafin bikin.
Majalisar Masarautar Bichi a wata wasiƙa ta hannun Sakataren Masarautar, mai kwanan wata 2 ga Fabrairu, 2024, ta sanar da gwamnatin jihar game da shirin gudanar da bikin naɗin sarauta mai cike da tarihi wanda aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga Maris, 2024.
Bikin, wanda shi ne irinsa mafi girma a Masarautar, za a yi shi ne don ɗaukaka Hakimi, Alhaji Salisu Ado Bayero tare da ba wa wasu fitattun ’yan asalin jihar sarauta na musamman na gargajiya.
Sai dai gwamnatin jihar ta bayar da umarnin dakatar da bikin a matsayin martani ga masarautar Bichi a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 21 ga watan Fabrairu mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar ƙananan hukumomi, Ibrahim M Kabara a madadin kwamishina, wanda kuma shi ne mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
