Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirin tallafa wa hanyoyin yaɗa labarai a taron SNB 

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta ci gaba da inganta ɗabi’a da ƙwarewar aikin jarida a Nijeriya, yayin da ƙungiyar Society of Nigerian Broadcasters (SNB) ta kammala taron ƙasa na biyu da bikin shigar da sababbin mambobi a Kano.

Taron, wanda ya ɗauki taken “ƙa’idojin Aikin Jarida da ƙwararru a Zamanin Fasahar Artificial Intelligence (AI),” ya tattaro manyan ƙwararru a harkar watsa labarai, jami’an gwamnati, masana, da shugabannin masana’antu domin tattauna ƙalubalen da sabuwar fasaha ke haifarwa ga aikin watsa labarai.

A jawabin Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Darakta Janar na Yada Labarai na Fadar Gwamnati Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wakilta, ya ce gwamnatin Kano ta dauki matakai na musamman domin haɓaka aikin jarida da ƙwarewar matasa.

Ya bayyana cewa gwamnatin ta kafa cibiyoyi guda uku da ke aiki cikakke domin horar da masu sha’awar sana’ar watsa labarai:

Cibiyar Bunƙasa Aikin Jarida a ARTV; Cibiyar Kula da Shirin wallafa Fina-Finai a Tiga da  Cibiyar Fasahar Sadarwa (IT) a Kura.

Ya ce wadannan cibiyoyin na taimakawa matasa su samu fasaha ta zamani da kuma zama masu dogaro da kai.

Bature ya kuma bayyana cewa a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Legas a 2025, gwamnatin Kano ta bukaci NBC ta ƙara tsaurara ka’idojin tace abun da ke fita ta kafafen intanet, musamman na siyasa da na addini da ke haddasa tashin hankali.

“A wajen taron, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan bayanai ya bayyana cewa aikin duba dokar NBC na tafiya, kuma Kano ta shirya gabatar da muƙalarta.”

Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnati na shirye ta ci gaba da aiki tare da kafafen watsa labarai domin gina al’umma mai tarbiyya da fahimtar juna.

Ya kuma tunatar da wasu daga cikin lambobin yabo da ya samu daga jaridun ƙasa, ciki har da Gwamna Mafi Kyau ga ‘Yan Jarida na 2025, wanda ƙungiyar NUJ ta ba shi a shagulgabanta na shekara 70.

A nasa ɓangaren, Shugaban SNB kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Federal University Kashere, Farfesa Umar Pate, ya nuna godiya ga gwamnatin Kano bisa goyon bayan da ta ba wa taron.

“Muna alfahari da gudanar da wannan taro a Kano, inda aikin rediyo ya fara a Nijeriya tun a shekarar 1940. Ba zai yiwu mu yi taron nan ba da babu goyon bayan gwamnatin Kano.”

Farfesa Pate ya jaddada bukatar kiyaye gaskiya, ingancin abun da ake watsawa, da ka’idojin aiki a zamanin bayanai marasa tushe da ka iya yaɗuwa cikin daƙiƙa.

Fitaccen ɗan jarida kuma tsohon mai gabatar da shirye-shirye, Ahmad Aminu, ya waiwayi tarihin watsa labarai a Nijeriya tun daga 1932. Ya ja hankalin cewa dogaro da AI fiye da kima na iya rage ƙirƙira da ɗabi’ar sana’a.

Ya ce, “AI na taimako sosai, amma amfani da shi ba daidai ba zai iya haifar da lalaci da rikice-rikice.”

Sauran jawaban sun fito daga: Usman Shehu, Kwamishinan Bayani na Bauchi, wakilin Gwamna Bala Mohammed, Farfesa Usman Tar, Kwamishinan Bayani na Borno, wakilin Gwamna Babagana Umara Zulum, Yemisi Bamgbose, Sakatare na ƙungiyar BON da Dr. Garba Ubale Dambatta, Janar Manaja Pyramid FM, wakilin Darakta Janar na FRCN da Sani Balarabe, Mataimakin Darakta na Digital Media, Voice of Nigeria (VON).

Dukkansu sun bukaci tsaftace fagen watsa labarai, tare da tabbatar da cewa ƙwararru na bibiyar ka’idojin aiki musamman a daidai lokacin da fasahar AI ke ƙara tasiri.

An kammala taron da shigar da sababbin mambobi da ziyarar aikin gadar ɗan’Agundi dake ƙaramar hukumar Binni tare da taron liyafar cin abinci don girmama baƙi.

Taron ya kare da shigar da sababbin mambobin SNB daga shiyyoyi guda shida na kasar idan Kuma dukkan mahalarta Taron suka nufi Gurin da ake aikin Gadar Dan’Agundi dake Karamar hukumar Binni da Liyafar cin Abinci. Bikin shigarwar ya gudana ta wajen taro da kuma hanyar intanet (virtual).

By ukarofi