
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kano ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama daga ƙungiyoyin addinin Musulunci game da kalaman Sheikh Lawal Triumph a Kano.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf bayan tantance takardun ƙorafe-ƙorafen, ya umarci a miƙa su ga Majalisar Shura ta jihar domin gudanar da aiki akansu.
A wata takarda da Sakataren yaɗa labarai na Sakataren gwamnatin, Musa Tanko ya fitar, ya ce an samu takardun ƙorafe-ƙorafen ne daga ɓangarori kamar haka:”
- 1. Safiyatul Islam of Nigeria
2. Tijjaniya Youth Enlightenment Forum
3. Interfaith Parties for Peace and Development
4. Sairul Qalbi Foundation
5. Habbullah Mateen Foundation
6. Imams of Juma’at Mosques under Qadiriyya Movement
7. Committee of Sunnah Preachers, Kano
8. Multaqa Ahbab Alsufiyya”
Alhaji Umar Farouk, wanda shi ne Sakataren gwamnatin (SSG) a madadin gwamnatin, ya umarci da a miƙa su ga majalisar domin yin nazari akansu tare da fitar da sakamako.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin ta cigaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna a tsakanin baki daya ƙungiyoyin al’ummar musulmi da ke jihar.
