’Yan wasa biyar da suka fi yawan lashe kyautar Ballon d’Or a tarihin ƙwallon ƙafa

Spread the love

Kyautar Ballon d’Or, wacce Hukumar ƙwallon ƙafar Faransa ta kafa a 1956, ita ce kyauta mafi girma da ake ba ɗan wasan ƙwallon ƙafa, wacce ke nuna maƙurar ƙwarewar ɗan wasa.

A tsawon tarihin ba da wannan kyauta, akwai fitattun ‘yan wasa biyar da suka lashe ta sau uku ko fiye da haka, alamar da ke nuna ƙwarewarsu a tarihin fagen ƙwallon ƙafa.

’Yan wasan ƙwallon kafa biyar ne suka taɓa lashe kyautar Ballon d’Or sau uku zuwa fiye da hakan a tarihi.

Jaridar Blueprint Manhaja ta yi nazari kan ‘yan wasan da suka fi yawan kyautar Ballon d’Or, tun daga kafa ta, har zuwa ranar 22 ga Satumba, 2025 da aka samu sabon gwarzo – Ousmane Dembele.

An gudanar da taron ba da kyautar Ballon d’Or ta 2025 ne a Paris, inda fitaccen ɗan wasa, Ousmane Dembele ya samu kyautar a karon farko.

Ga jerin ‘yan ƙwallon da suka fi kowa yawan lashe kyautar Ballon d’Or:

1. Lionel Messi:

Lionel Messi shi ne kan-gaba a jerin ‘yan ƙwallon kafa da suka lashe kyautar Ballon d’Or, inda ya lashe kyautar har sai tawas.

Messi ya lashe Ballon d’Or a shekarun: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021, da kuma 2023.

Ba sai an faɗa ba, tuni duniya ta shaida cewa Messi, ɗan asalin Argentina, ya kasance ɗan wasa mai hazaƙa, iya taka leda da kuma zura ƙwallaye.

Messi ya lashe mafi yawan kyautar Ballon d’Or a lokacin da yake buga wasa a Barcelona, inda ƙwarewarsa a buga tamaula ya sa ƙungiyar ta lashe kofin Zakarun Turai a lokuta daban-daban.

A shekarar 2021 ne Messi ya lashe Ballon d’Or, lokacin yana buga wasa a Paris Saint-Germain (PSG), sai kuma 2023 da ya lashe kyautar bayan Argentina ta lashe kofin duniya.

2. Cristiano Ronaldo:

Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar a tarihi.

Cristiano Ronaldo ne ke biya da Messi, bayan da ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar, watau a shekarun 2008, 2013, 2014, 2016, da 2017.

ɗan wasan na Portugal, ya kasance ƙwararre a fagen ƙwallon ƙafa, kuma yadda ya yi fice a zura ƙwallaye a ragar abokan hamayya, ya sanya shi ya zamo babban ɗan wasa.

Ronaldo ya fi lashe kyautar Ballon d’Or a lokutan da yake taka leda a Manchester United da kuma Real Madrid, inda ya lashe kyautar a 2016 da 2017 saboda nasarar da ya samu a gasar Zakarun Turai.

Duk da yana da shekaru 40, yadda Ronaldo yake ci gaba da buga wasa a gasar Saudi Pro League ya nuna ƙwazonsa, amma dai har yanzu akwai tazara tsakaninsa da Messi a ɗaukar Ballon d’Or.

‘Yan wasan ƙwallo uku masu Ballon d’Or uku-uku:

Kafin Messi da Ronaldo, rahoton UEFA ya nuna cewa ‘yan wasa uku ne kawai suka taɓa lashe kyautar Ballon d’Or da ta kai sau uku:

3. Johan Cruyff (1971, 1973, 1974)

4. Michel Platini (1983, 1984, 1985)

5. Marco van Basten (1988, 1989, 1992)

Tsarin da Cruyff ya kawo na wasan “Total Football” sun sauya ƙwallon ƙafa, yayin da basirar Platini a tsakiyar fili ta ƙara wa Juventus ƙarfi.

Kwazon Van Basten na zura ƙwallaye ne ya sanya ya yi fice a zamaninsa, duk da cewa yawan raunuka ya kawo ƙarshen buga ƙwallonsa da wuri.

A ‘yan shekarun nan, an samu ɓullar sababbin jini a harkar buga ƙwallo. Kamar Kyalian Mbappe, wanda ya lashe Ballon d’Or a 2024 a karon farko, bayan nuna bajinta a PSG da Faransa.

Ousmane Dembele ya lashe Ballon d’Or na bana:

Ousmane Dembele, ya lashe kyautar Ballon d’Or a karon farko, bayan kwarewarsa da ta taimakawa PSG ta lashe kofin zakarun Turai.

Dembele ya lashe wannan kyauta ta Ballon d’Or, a matsayin zakaran ɗan wasan kwallon kafa da ya fi kowane ƙoƙari a maza a kakar wasan da ta gabata.

Dan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon kafa ta PSG ya samu wannan nasara ne bayan doke matashin ɗan wasan Barcelona, watau Lamine Yamal.

By ukarofi