Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Dr. Usman Bugaje, ya yi martani kan iƙirarin tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Aremu Obasanjo, na cewa bai nemi tazarce karo na uku ba.
Bugaje ya jaddada cewa tsohon shugaban ƙasar ya yi duk mai yiwuwa domin tsawaita zamansa a kan mulki.
Dr. Usman Bugaje ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin ‘Morning Show’ na tashar Arise tɓ ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.
A makon da ya gabata a wani taron tattaunawa kan dimokuraɗiyya da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a ƙasar Ghana, Obasanjo ya yi watsi da batun wanda ya daɗe tana jawo cece-kuce.
Obasanjo ya bayyana cewa bai taɓa neman wa’adin mulki na uku ba.
Bugaje wanda ya kasance ɗan majalisa a lokacin mulkin Obasanjo, ya dage cewa ‘yan majalisu a wancan lokaci suna da masaniya game da shirin neman wa’adin mulki na uku.
“Zan iya tabbatar maka cewa Obasanjo ya nemi wa’adin mulki na uku. Ya yi duk abin da zai iya a ƙarƙashin ikonsa domin samun wa’adin mulki na uku, amma ya kasa cimma hakan,” inji Bugaje.
Tsohon ɗan majalisar ya ce hujjar Obasanjo ba ta da ƙarfi, inda ƙara da cewa wakilan Obasanjo sun yi barazana ga ‘yan majalisa da dama a lokacin.
“Yanzu, kawai saboda bai ɗauki waya ya kira wani kai tsaye ba, ba hujja ba ce cewa bai nemi wa’adin mulki na uku ba.
“Kawai basaja ne amma mu a Majalisar Tarayya a wancan lokacin mun san babu wata shakka cewa ya yi aiki dare da rana don cimma wannan buri, kuma da yawa daga cikinmu mun fuskanci barazana daga wajen wakilansa.”
Bugaje ya kuma tuno barazanar da aka yi wa ‘yan majalisa, inda ya kawo misali da Sanata ɓictor Lar, wanda a wancan lokaci ya kasance shugaban ‘yan majalisar wakilai na Arewa.
Ya ce, an tilasta masa yin ɓuya a lokuta daban-daban kafin taron karshe da aka yi don kaɗa ƙuri’ar ƙin yarda da shirin wa’adin mulki na uku.
“Waɗanda suka rarraba kuɗin, waɗanda aka ba su kuɗin, da kuma waɗanda suka ƙi karɓar kuɗin duk suna raye. Akwai kwakkwaran shaida, wannan magana ba za a iya musanta ta ba. Babu yadda zai yi ya ce bai nema ba,” inji Bugaje.
