DSS na yunƙurin sake gabatar da hujja akan shari’ar badaƙalar kuɗin makamai na Dasuƙi bayan shekaru

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A wani yunƙuri na cigaba da gudanar da shari’ar tsohon Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Kanal Sambo Dasuƙi (mai ritaya) bayan shekaru goma, Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake gabatar da hujjojin da kotu ta yi watsi da su a baya.

Lamarin da ofishin tsaro ya yi watsi da shi bayan bayyana shi a matsayin baƙon abu da doka ba ta san da shi ba, wanda hakan ya sa Alƙali Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2025.

Hakan na zuwa ne kwanaki ƙadan da shari’ar ta samu tsaiko bayan da shaidar ɓangaren da ya shigar da ƙara ya gaza bayyana a gaban kotu duk da umarnin alƙalin na a kammala shari’ar zuwa ƙarshen watan nan na Satumba.

DSS, ta lauyan da ke kare ɓangarenta Oladipupo Okpeseyi (SAN), ta nemi kotun da ta yi nazari akan motoci 11 da aka yi zargin ƙwato su daga gidan Dasuki na Abuja yayin wani bincike a 2015.

An ajiye su ne tsawon shekaru goma a ofishin DSS, waɗanda ɓangare ne na hujjar da aka gabatar wa kotu da ta ƙi karɓa su a baya saboda rashin hujja mai ƙarfi akansu.

Saidai, a yanzu, Okpeseyi ya ce sun samu hujja mai ƙarfi da za su gabatar, wanda a cewarsa suna ƴancin yin hakan saboda doka ta ba su dama.

Lamarin da lauyan da ke kare Dasuƙi, wato A.A. Usman ya sa ya zargi ɗaya ɓangaren da yunƙurin dawo da abinda ya wuce, inda ya ce hakan zai karɓu ne kaɗai yayin da kotun gaba ta karɓi shari’ar.

A halin yanzu ido na kan hukuncin da kotun za ta yi a watan Oktoba musamman bisa la’akari da ko hujjar da aka gabatar a 2015 da aka faro shari’ar wajen ganin ko za ta yi aiki.

By Babaji