Gwamnatin Katsina ta buƙaci a soke jarrabawar WAEC ta Turanci

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Umar Raɗɗa a ranar Asabar ta buƙaci a soke jarabawar harshen Turanci da hukumar jarabawa ta yammacin Afirka wato WAEC ta gudanar a wannan makon.

Wannan kiran ya biyo bayan wani lamari da ya haifar da jinkiri mai tsawo kafin fara jarabawar a faɗin ƙasar.

Iyayen ɗalibai sun koka game da yadda aka bar yaransu cikin halin rashin tabbas a ranar Larabar a yayin da ɗaliban ke rubuta jarabawar Turanci.

Matsayar gwamnatin jihar ta fito ne daga bakin Kwamishinar Ilimin Firamare da Sakandare, Zainab Musa-Musawa, lokacin da ta kai ziyara ofishin WAEC da ke Katsina.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wannan matsaya ta samo asali ne daga wata takardar ƙorafi da babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Ummukhair Ahmed ta sanya wa hannu.

A baya dai, WAEC ta danganta jinkirin fara jarabawar da ƙoƙarin ta na hana maguɗin jarabawa, musamman yaɗuwar takardun jarabawar kafin lokacin farawa.

By ukarofi