Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ma’aikata na Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, ya rufe taron na kwanaki uku da aka shirya wa ma’aikatan gwamnatin jihar domin ƙara musu ƙwarewa a harkokin gudanar da aiki.
Da yake jawabi wajan rufe taron,shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa wannan horo wani muhimmin ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Jihar Katsina na inganta tsarin gudanar da ayyukan gwamnati tare da ƙara wa ma’aikata ƙwarewa da nagarta a aikinsu.
Ya jaddada cewa horon zai taimaka wajen samar da ingantaccen aiki, gaskiya da riƙon amana a ofisoshin gwamnati.
Alhaji Falalu Bawale ya kuma yaba wa ma’aikatan da suka halarci horon bisa irin jajircewa da kulawar da suka nuna a tsawon kwanaki ukun da aka ɗauka ana gudanar da horon.
Ya buƙace su da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen kyautata ayyukansu domin amfanin al’umma da ci gaban jihar baki daya.
Har ila yau, wasu daga cikin masu gabatar da horon sun yi ƙarin haske kan muhimman darussan da aka koyar, wadanda suka hada da tsarin sarrafa aiki na zamani, kyakkyawar mu’amala da jama’a, da kuma dabarun inganta aiki cikin sauri da inganci.
A ƙarshen taron, an gabatar da takardun shaidar kammala horo (satifiket) ga ma’aikatan da suka halarci horon na tsawon kwanaki uku, inda mahalarta suka nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa samar da wannan dama ta ƙara ilimi da ƙwarewa.
