Sanata Marafa ya koma ADC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sanata Kabir Garba Marafa ya shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance, a matsayin wani ɓangare na tafiyarsa ta siyasa don tsayawa takarar kujerar gwamna a Zamfara a shekarar 2027.

Ya yi kira ga magoya bayansa da su yi rijista da jam’iyyar.
Shiga Jam’iyyar ta ADC da Sanatan ya yi ta haifar da sha’awa sosai, inda magoya baya da yawa suke yin gaggawar yin rijista da Jam’iyyar ta ADC a Jihar Zamfara gabanin zaɓen da ke tafe.

A cewar Shugaban ƙungiyar magoya bayan Sanata Marafa, Alh. Surajo Garba Maikatako, Marafa ya jaddada muhimmancin zama memba don samun samun Nasarar Jam’iyyar ta ADC da Kuma kyakkyawar makomar Najeriya.

“Muna kira ga magoya bayanmu da su yi rijista cikin lumana kuma bisa doka.” Ya ce

“Muna kallon Jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyya mai gaskiya, adalci, da ingattar manufar dimokuraɗiyya.” Maikatako ya bayyana

Ana ganin matakin Sanatan a matsayin wani babban ci gaba ga ADC, inda mutane da yawa suka yi imanin cewa zai taka muhimmiyar rawa a nasarar jam’iyyar a 2027 a jihar Zamfara.

By ukarofi