Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da kayayyakin wasanni domin inganta harkokin wasanni, motsa jiki da kuma bunƙasa hazakar ɗaliban makarantu masu buƙata ta musamman a faɗin jihar.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ɗakin taro na filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina.
Babban sakataren ma’aikatar matasa da wasanni, Alhaji Muhammad, ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne a ƙoƙarin gwamnati na bai wa dukkan yara damar nuna ƙwarewarsu, musamman masu buƙata ta musamman.
Ya ƙara da cewa samar da kayayyakin zai taimaka wajen ƙarfafa gwiwar ɗaliban tare da ba su damar bunƙasa baiwarsu domin amfanin kansu da al’umma baki ɗaya.
A nasa ɓangaren, daraktan wasanni na Jihar, Alhaji Abdullahi Bello Rawayau, ya ce wannan mataki zai haɓaka harkokin wasanni a tsakanin waɗannan dalibai, yana mai jaddada muhimmancin wasanni wajen gina jiki da tarbiyya.
Bikin ya samu halartar jami’ai, malamai da masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi da wasanni.
Kayayyakin sun haɗa da riguna,kwallaye,takalma da sauransu.
