Majalisar Ɗinkin Duniya ta yaba wa shirye-shiryen cigaban Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Mataimakiyar Sakatare Janar a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), Amina Mohammed, ta ce Jihar Zamfara a buɗe take kuma mai sauƙin shiga, kuma Majalisar Dinkin Duniya tana son zama abokiyar hulɗa da gaske ga Jihar.

Mataimakiyar Sakatare Janar ta MDD ta yi wannan tsokaci ne yayin da ta kai ziyara a Jihar ta Zamfara a ranar Alhamis.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta lura cewa Mataimakiyar Sakatare Janar ta gudanar da wani bincike a wurin a ƙaramar hukumar Maru da sauran wurare.

Sanarwar ta ƙara da cewa tawagar Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ta haɗa da wakilin UNDP, Elsie Attafuah, da babbar mataimakiyar musamman ga Mataimakiyar Sakatare Janar, Hadiza Elayo.

Sauran su ne shugabar UNODC, Cheikh Toure; Shugabar ƙasa, UNICEF, Wafaa Saeed; shugabar ƙasa, IOM, Sharon Dimanche; Shugabar Ƙasa, UNHCR, Arjun Jain; Shugabar Ƙasa, UNAIDS, Krittayawan Boonto; da Shugaban Ƙasa, UNFPA, Francis Kuawu.

A lokacin taron tattaunawa na ɓangarori daban-daban da Jihar Zamfara, Gwamna Lawal ya bayyana shirye-shiryen gwamnatinsa na ciyar da Jihar gaba mai ɗorewa, juriyar yanayi, da ci gaban haɗaka ta hanyar haɗin gwiwa na dabarun zamani.

Gwamnan ya ce Zamfara tana kan wani lokaci mai kyau, tare da yawan jama’a miliyan 5.3, kuma tattalin arzikin jihar yana kan noma ne, inda kashi 82% na al’ummarta suka dogara da noma. “Ajandar ceto maki shida ta Zamfara dabara ce da aka tsara don daidaita, sake ginawa, da kuma sauya jihar zuwa ga ci gaba mai ɗorewa.” Inji gwamnan

Mataimakiyar Sakatare Janar a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta nanata cewa gabatarwar da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi a bayyane take. “Wannan ya isa mu sami damar yin haɗin gwiwa.

“Masu zuba jari suna son muhalli mai kyau, zaman lafiya shine abin da kuke buƙata a yau ga mutane su zo, labarin Zamfara ya mayar da hankali kan rikici da ya shafi ma’adanai masu ƙarfi, kuma wannan yana buƙatar canzawa.

“Abin da kuka nuna mana a yau, da farko dai, sha’awarku ga abin da kuke so mu yi, kuma wannan shine abin da masu zuba jari ke so, Suna son sanin abin da kuke so.

“Ina farin cikin kasancewa a nan Zamfara a yau, domin ina son in nuna wa duniya cewa ya kamata mu mai da hankali kan abin da ke faruwa a matakin gida. Domin a nan ne mutane suka fi rauni, inda shugabanci ya fi rauni, kuma inda akwai ƙarancin albarkatu.

“Lokacin da muka ziyarci Jihar Zamora, muna jinjinawa ga ƙoƙarin da aka yi da kuma tasirin abin da ke faruwa a wasu wurare a duniya ga mutanen da ba su da alaƙa da abin da ya haifar da shi tun farko.

“Jihar Zamfara tana da sauƙin shiga a yau. Kuma za ta fi sauƙin shiga saboda har yanzu ana kan gina hanyar da muka yi tafiya a kai. Idan aka gama ta, za ta farfaɗo da harkokin kasuwanci da kasuwannin da ke kewaye da ita, kuma da fatan, nan da nan, za mu ga ƙarin zaman lafiya.

“Ina ganin haƙar ma’adinai, ina ganin damarmaki, ina ganin kasuwa da buƙata, amma kuma ina ganin shugabannin da ke nan waɗanda ke son duba cibiya, tsarin aiki da abokannin tarayya don kammala aikin. “

“Akwai muhimmiyar dama a nan. Dole ne kowa ya taka rawa, wannan ba abu ne da gwamna zai yi shi kaɗai ba, Majalisar Ɗinkin Duniya tana son zama abokiyar hulɗa ta gaske ga Jihar Zamfara.” In ji ta.

By ukarofi