Borno: Boko Haram ta fitar da bidiyon ‘yan Ngoshe 416 da ta yi garkuwa da su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsagin Jama’atu Ahlis-Sunna Lidda’Awati Wal-Jihad da aka fi sani da Boko Haram, ya fitar da bidiyon da ke nuna halin da mutane 416 da suka sace a Ngoshe, wani ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno ke ciki sama da wata guda da harin yankin.

A faifan na tsawon minti shida da daƙiƙu 43 da aka fitar a ranar Alhamis ƙungiyar ta nuna yare fa yin hira da mutanen, waɗanda galibinsu mata ne da yara da maza kaɗan acikinsu.

An ga yadda suke roƙon gwamnatin Nijeriya da ta amince da buƙatun ‘yan ta’addan domin su samu ‘yanci daga hannunsu.

Haka kuma an ga mayaƙan Boko Haram ɗin riƙe da manyan makamai a kewaye da waɗanda aka kama.

Wakilin mayaƙan da ya yi magana da harshen Hausa, ya ce sun fitar da bidiyon ne domin nuna wa duniya cewa mutanen suna nan a raye kuma ba a cutar da su ba.

Wata mata da ta yi magana a madadin sauran ta tabbatar da cewa ana ba su abinci, matsuguni, da magani ga waɗanda suka ji rauni.

Saidai ta ce suna cikin matsananciyar damuwa da fargaba sakamakon kisan wasu danginsu da aka yi lokacin da wani jirgin yaƙi ya kai hari, sannan tana son su koma gidajensu domin rayuwar dajin ta bambanta da wadda suka saba.

Akan haka ne ta kirayi Mai Girma Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Sanata Ali Ndume da Ciyaman ɗin Gwoza da su gaggauta kawo musu ɗauki.

A ranar 4 ga watan Maris, 2026 ne ‘yan ta’adda suka kai wani hari a sansanonin soji da na ‘yan gudun hijira a yankin Ngoshe, inda suka halaka sojoji da fararen hula, ƙone motocin yaƙi da yin awon-gaba da mutane da dama.

Tuni dai Ƙungiyar Matasan Borno ta Kudu BOSYA, ta tabbatar da al’amarin ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Samaila Kaigama, yana mai cewa ƙungiyar ta shiga tsakani ne domin ba wa waɗanda aka sace murya da kuma ƙoƙarin samar da mafita ta dindindin game da rashin tsaro a kudancin Borno.

By Babaji