Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kayayyakin sun haɗa da buhunan hatsi guda 7,000 da aka raba wa ƴan gudun hijira da marasa galihu da ambaliyar ruwan sama ya shafa.
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka a lokacin da ya ke bayyana wa manema labarai nasarorin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta samu tun lokacin hawan hawansa mulki.
Ya ce wannan ƙari ne akan kuɗi Naira miliyan 451 da aka raba wa wasu ƙarin mutane dubu ɗaya.
Bugu da ƙari kuma malam Joɓe ya ce an raba wasu kayan agaji na kuɗi Naira miliyan 200 ga marasa galihu domin rage masu raɗaɗin asarar da suka yi.
Duba da halin ƙuncin rayuwa da aka faɗa, mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta sayi hatsi buhu 95,000 inda su ma ƙananan hukumomi 34 suka sayi hatsi buhu 75,000 inda aka sayar wa al’ummar jihar bisa rabin farashin da aka saya.
Haka kuma Malam Joɓe ya ƙara da cewe a ƙudirin gwamnati na kawo sauƙi ga al’umma, gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan 2 wajen sayo buhunan shinkafa mai nauyin kilogram 50 guda 40,000 wanɗanda aka raba wa marasa galihu tare da Naira 10,000 ga kowannen su.
“Ganin kusan duk al’ummar jihar musulmai ne gwamnatin Dikko Raɗɗa ta samar da cibiyoyin cin abinci guda 361 na ciyar da mutane 200 a kowacce unguwa lokacin watan azumi da ya wuce”, inji mataimakin gwamnan.
“Gwamnatin Katsina da haɗin-gwiwa da hukumar bunƙasa ƙananan sana’o’i (SMEDEN) ta bude cibiyar ci-gaban masana’antu a unguwar Tudun Matawalle a garin Katsina a matsayin wurin kasuwancin kayan kwalliya, ayyukan fata da harkokin noma.”
Haka kuma Malam Joɓe ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe kudin fiye da Naira biliyan 8 wajen tallafa wa magidanta da marasa galihu a faɗin jihar.
Mataimakin gwamnan ya nanata ƙudirin gwamnatin jihar wajen aiwatar da ayyuka da shirye-shirye da suka shafi inganta rayuwar al’ummar jihar.