Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), ta sake naɗa Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Darakta-Janar a karo na biyu.
WTO ta wallafa hakan ne a shafinta na X, a ranar Juma’a inda Majalisar Zartarwarta ta ce naɗin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025.
Majalisar ta ce ta amince da naɗa ƴar Nijeriyar ne na wani zangon shekara huɗu sakamakon ƙwarewarta ta fuskar jagoranci da hangenta game da samar da gobe mai kyau ga WTO.
Hakan na zuwa ne kasancewar ba a samu wani da ya nemi a ba shi muƙamin ba bayan Okonjo-Iweala wadda musamman majalisar ta zaɓe ta.
Majalisar ta kuma yaba mata game da himma da take bai wa harkokin hukumar wajen samar da ci-gaba.
A ranar 1 ga watan Maris, 2021 ne Okonjo-Iweala ta zama mace farko kuma yar Afirka ta farko da ta samu muƙamin Darakta-Janar inda kuma wa’adin nata na farko zai ƙare a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.