Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi kira ga waɗanda ke shirin haddasa tashin hankali da su zabi hanyar tattaunawa, yana mai jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya, adalci da daidaito ga kowa da kowa. Gwamnan ya yi wannan kiran ne a Birnin Gwari ranar Alhamis, yayin da ya karɓi tubabbun ‘yan bindiga da kuma buɗe kasuwar dabbobi da aka rufe tsawon shekara goma saboda matsalar tsaro.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna, tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tarayya, sun kafa kwamitin tattaunawa da zaman lafiya wanda ke aiki tare da masu ruwa da tsaki. Ya ce ta hanyar taruka da tattaunawa masu zurfi, gwamnatinsa ta haifar da yadda, inda manyan shugabannin ‘yan bindiga da mabiyansu da dama suka ajiye makamai suka rungumi zaman lafiya.
Ya kuma bayyana cewa mutanen da suka tuba suna samun horo na musamman a cikin shirin gyaran hali da gwamnatin jihar Kaduna ta ƙirƙiro tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya. “Wannan shiri yana bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na kwace makamai, rushe ƙungiyoyin ta’addanci da sake mayar da waɗanda suka tuba cikin al’umma domin su zama ‘yan ƙasa masu amfani,” in ji shi.
Gwamnan ya yi gargaɗi cewa shirin gyaran halin tubabbun ‘yan bindiga yana bin tsarin “kyauta da hukunci,” inda ya bayyana cewa yayin da gwamnatin za ta karɓi waɗanda suka zaɓi zaman lafiya, ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ɗaukar mataki mai tsanani kan waɗanda suka ci gaba da aikata laifuka.
Haka kuma, ya bayyana cewa hukumomin tsaro da leƙen asiri sun sami gagarumar nasara wajen murƙushe manyan shugabannin ‘yan bindiga, rushe ƙungiyoyi masu aikata laifuka da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su. Wannan, a cewarsa, na daga cikin ƙoƙarin da ake yi don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Kaduna.