Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Wakilai ta yi kira ga Ma’aikatar Ilimi da ta samar da shiri da zai bada damar a sanya koyar da yarukan gida a cikin jaddawalin karantarwa a makarantun Nijeriya don amfani da su a matsayin karɓaɓɓu.
Haka na zuwa ne bayan da ɗan Majalisa Kalejaiye Adeboye Paul (APC Legas) ya ɗauki nauyin batun a zauren majalisar, ya na mai nuna muhimmancin hakan a makarantun firamare da ƙaramar sekandire.
Ya ce Nijeriya ƙasa ce mai arziƙin yaruka daban-daban gami da al’adu masu ƙarfi don akwai buƙatar a faɗaɗa karɓaɓɓun yaruka bayan Turanci.
Ya kuma ce turanci da ake amfani da shi a matsayin karɓaɓɓe a ƙasar, ya ɓoye Hausa da Igbo da Yaroba waɗanda su ne asalin yarukan ƙasar.
Ya ƙara da cewa, koyar da yara harshen uwa shi ne ke sanyawa a samu alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɗalibi da malaminsa wanda hakan zai taimaka wajen samar da yanayin karatu mai kyau.
Har’ilayau, ɗan majalisar ya ce fifita yarukan gidan zai taimaka wajen inganta ƙabilu da harkokin ilimi da makamantansu.