Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta bai wa kwamitin da ta kafa domin binciken zargin cin zarafi da wata baturiya ‘yar ƙasar waje da ya shafi Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, wa’adin makonni huɗu domin gabatar da rahotonsa.
Bayanin haka na cikin sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na Jihar Katsina, Dr. Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Laraba, 25 ga Nuwamban 2026.
Sanarwar ta ce kwamitin mai mambobi 9, ƙarqashin jagorancin Mai Shari’a Amiru Sanusi mai ritaya, zai binciki zargin, tare da gayyatar duk mutanen da ke da alaƙa da lamarin domin bayar da bayanai.
Haka kuma, kwamitin zai binciki dalilin ziyarar baturiyar mai yawon buɗe ido zuwa fadar Sarkin Daura, ya duba hujjoji da takardun da suka shafi lamarin, sannan ya gabatar da shawarwari kan matakan da suka dace bisa sakamakon binciken sa.
Gwamnatin ta buƙaci jama’a su guji tsoma baki a binciken, tare da bayyana cewa wa’adin makonni huɗun zai fara ne daga ranar ƙaddamar da kwamitin.
