Gwamnatin Katsina za ta ɗauki nauyin likitoci zuwa ƙasashen waje domin samun horo

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na karfafa tsarin kiwon lafiya a jihar ta hanyar gina ƙwarewa mai ɗorewa, ciki har da ɗaukar nauyin likitocin gida domin samun horaswa ta musamman a ƙasashen waje.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbaci ne a yayin bikin karrama ‘Revive Belgium Mission’, bayan kammala aikin jinya kyauta na tsawon mako biyu da suka gudanar a Jihar Katsina, inda aka bai wa dubban al’umma kulawar lafiya ta musamman.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan shiga tsakani a matsayin abin yabo matuƙa kuma babbar hidima ga bil’adama, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar a shirye take ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da tawagar Belgium domin samar da tasiri mai ɗorewa.

“Mun shirya ɗaukar nauyin likitocinmu zuwa ƙasar Belgium domin su samu ƙwarewa ta zamani domin su koyar da wasu a nan. Wannan ita ce hanyar da za mu tabbatar da ɗorewar ilimi da ƙwarewa,” in ji Gwamnan.

Ya jaddada cewa ɗorewa ita ce ginshiƙin manufofin gwamnatinsa a ɓangaren kiwon lafiya, ta hanyar horaswa mai ci gaba, kayan aiki na zamani, da ƙwarewar fasaha.

“Ba wai kawai tsoma bakin na ɗan lokaci ba, burinmu shi ne gina tsare-tsare da za su ɗore suna ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummarmu,” ya ƙara da cewa.

Dangane da mataki na gaba, Gwamnan ya bayyana cewa haɗin gwiwar za ta mayar da hankali a kan gano cutar kansa da maganinta, musamman cutar kansar nono.

“Gwamnatin Jihar Katsina za ta bayar da cikakken goyon baya ga aikin kansa da ke tafe. Ganowa da wuri da kuma magani cikin lokaci suna da matukar muhimmanci, kuma mun ƙuduri aniyar cimma wannan buri,” Dikko ya ce.

Gwamna Raɗɗa ya kuma sanar da shirin ƙulla yarjejeniyar fahimta (MoU) domin samar da tsari na dindindin ga haɗin gwiwar.

Haka kuma, ya bayyana cewa jihar na gina cibiyar ɗaukar hoton bincike ta zamani wadda za ta ƙunshi na’urorin bincike na zamani, wacce ake sa ran za ta kasance cikin mafi inganci a ƙasar nan.

“Wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen horas da likitocinmu kan amfani da kayan bincike na zamani domin tabbatar da ingantaccen amfani da kuma sahihin sakamakon bincike,” in ji shi.

Gwamnan ya sake jaddada hangen nesan gwamnatinsa na mayar da Katsina cibiyar kiwon lafiya, wadda za ta riƙa bai wa mazauna jihar da na jihohin makwabta hidimomin lafiya masu inganci.

“Manufarmu ita ce mu mayar da Katsina cibiyar kiwon lafiya da ke karɓar tura marasa lafiya, da kuma kulawar jinya ta zamani,” ya bayyana.

Ya ce haɗin gwiwar da Revive Belgium Mission ba wai tiyata kadai ba ce, har da kula da asibitoci, horaswa, bincike, da bunƙasa ƙwarewar ɗalibai da ma’aikatan lafiya.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa aikin jinyar ya zarce hasashe, inda aka wuce burin ayyuka da kaso 100 zuwa 200 cikin dari, kuma kashi 80 zuwa 90 cikin ɗari na waɗanda suka amfana sun fito ne daga yankunan karkara.

“Wannan aiki ya wuce dukkan burin da aka sa.Ga da yawa daga cikin wadanda suka amfana, wannan ita ce damar farko da suka samu na samun magani mai sauya rayuwa,” ya ƙara da cewa.

Duk da ƙalubalen da ɓangaren kiwon lafiya na jihar ke fuskanta, Gwamnan ya bayyana aikin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma ya yi tasiri sosai.

“Tsarin kiwon lafiyarmu har yanzu na buƙatar irin wannan gudunmawa na Revive Belgium Mission ta taimaka wajen cike giɓi masu muhimmanci a lokaci mai matuƙar muhimmanci,” in ji shi.

By ukarofi