
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, kuma sanannen Attajiri, Alhaji Aliko Ɗangote, ya sake tayar da kura kan rikicin da ke tsakaninsa da Malam Farouk Ahmed, Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Ƙasa da Rarrabawa (NMDPRA), inda ya yi zargin cewa rayuwar kuɗin da Farouk ke yi ba ta dace da adadin kuɗin shigar da ya ke samu ba.
Ɗangote ya ce ƴaƴan Farouk Ahmed su huɗu sun yi karatun sakandare a ƙasar Switzerland, inda ya ce an kashe kimanin Dala miliyan 5 kan karatunsu na sakandare kaɗai ba tare da haɗawa da na jami’a ba.
“Idan aka dubi albashinsa da kuɗin shigar da yake samu, ba zai yiwu ya ɗauki nauyin irin waɗannan kuɗaɗe ba. Ko da ni ne zan kashe dala miliyan biyar a cikin shekaru shida kan ’ya’yana huɗu, dole ne hukumar haraji ta binciki harajina da yawan kuɗin da nake biya,” in ji Dangote.
Ya ƙara da jaddada bambancin rayuwa tsakanin irin wannan kashe-kashe da halin da jama’a ke ciki, musamman a Jihar Sokoto, inda ya ce mutane da dama na fama da rashin kuɗin biyan kuɗin makaranta.
“A Sokoto, inda ya fito, mutane na ta gwagwarmayar biyan Naira 100,000 na kuɗin makaranta. Yara da dama suna zaune a gida ba sa zuwa makaranta saboda Naira 100,000,” in ji Dangote.
Dangote ya ce wadannan zarge-zarge na bukatar cikakken bincike, yana mai kira ga hukumomin da abin ya shafa da su binciki al’amuran kuɗin Farouk Ahmed domin tabbatar da Gaskiya da riƙon amana a harkokin gwamnati.
A cewarsa makarantun da ƴaƴan Farouk suak halarta sun haɗa da Montreux School, Aiglon College, Institut Le Rosey, da La Garenne International School waɗanda suka ɗauki tsawon shekaru shida suna zuwa.
Ya yk ikirarin aƙalla ana kashe jimillar kuɗin karatu da na jirgi da ya kai kimanin Dala 200,000 a kowace shekara, adadin da ya kai $800,000 na dukkaninsu. A jimillance kuma Dala miliyan 5 na ƴaƴa huɗun.
