Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sanar da ware Naira biliyan huɗu a matsayin gudunmawar gwamnatin jihar domin aiwatar da shirin tallafa wa mata na Najeriya (Nigeria for Women Project Scale-Up – NFWP-SU), wani shiri da Bankin Duniya ke tallafa wa da nufin inganta rayuwar mata ta hanyar bunƙasa tattalin arziƙi, koyar da tanadin kuɗi, haɓaka ƙwarewa da samar da tsarin haɗin kai a tsakanin al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar gani da ido da kuma bibiyar ayyukan shirin a ƙauyukan Tudun Wada da Sabon Garin Kalgo da ke ƙaramar hukumar Daura.
Ya bayyana cewa a halin yanzu ana aiwatar da shirin ne a ƙananan hukumomin Katsina, Daura da Funtua, tare da shirin faɗaɗa shi zuwa dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa kimanin mata 19,000 ne ake sa ran za su amfana da shirin a ƙaramar hukumar Daura kaɗai, ta hanyar kafa ƙungiyoyi 760, inda kowace ƙungiya take ƙunshe da mata 25. Ya ƙara da cewa mata masu cin gajiyar shirin a ƙananan hukumomi uku da aka fara da su sun tara sama da Naira miliyan 349 ta hanyar tsarin ajiyar kuɗi na mako-mako, lamarin da ke nuna nasarar shirin wajen ƙarfafa al’adun tanadi da dogaro da kai ga mata.
Gwamnan ya ce shirin na taimaka wa mata wajen samar da ɗorewar hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, ƙarfafa tattalin arzikin iyali da inganta rayuwarsu baki ɗaya. Ya yaba wa matan da suka rungumi shirin bisa jajircewa da nuna ƙwazo, tare da tabbatar musu da ci gaba da samun goyon bayan gwamnati. Haka kuma ya bayyana cewa za a haɗa maza a matakai na gaba domin ƙara faɗaɗa tasirin shirin ga al’umma.
Tun da farko, kwamishiniyar ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta yi wa tawagar gwamnan bayani kan nasarorin da aka samu tun bayan fara aiwatar da shirin, tare da jaddada ƙudirin ma’aikatar na tabbatar da cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankali yayin ziyarar har da yadda mata suka nuna a aikace yadda ake kafawa da kuma gudanar da ƙungiyoyin mata da ke ƙarƙashin shirin.
Taron ya samu halartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, shugaban ƙaramar hukumar Daura, sarakunan gargajiya, malamai, wakilan ofishin shirin na ƙasa da na jiha, da sauran manyan jami’an gwamnati.
