Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta yi kira ga waɗanda aka bai wa kwangilar gyare-gyaren wuraren da za a gudanar da bikin al’adu da kamun kifi na Argungu da su hanzarta su kammala ayyukansu cikin lokaci.
Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ne ya yi wannan kira a wani rangadin gani da ido a wuraren da za a gudanar da bukukuwan a garin Argungu.
Sanata Umar Abubakar ya ce ya kamata ‘yan kwangilar su yi aiki tuƙuru ba dare ba rana tare da tabbatar da sun yi aiki mai inganci bisa la’akari da ƙurarren lokaci da ke akwai.
Ya ƙara da cewa duk wanda aka bai wa wani aiki da ya shafi gyare-gyaren wuraren da za a yi amfani da su yayin bikin kamun kifin musamman waɗanda ba su fara aikin ba da su tabbatar da cewa sun soma aikin kafin ranar Litinin mai zuwa saboda ita kanta gwamnatin ba ba za ta zauna ba har sai ta ga an kyautata duk wuraren bisa ga la’akari da irin dubban al’ummar da za su zo daga sassan duniya don nuna irin ta su bajinta musamman wajen kamun kifi.
Haka-zalika mataimakin gwamnan ya yi kira ga al’ummar masarautar Argungu da su baiwa gwamnatin jihar Kebbi da masarautar Argungu haɗin kai don ganin an sami nasarar wannan bikin kamar yadda aka san su da karramawa da mutunta baƙi da kuma bin doka da oda.
