Wani bawan Allah ya bayar da Naira milliyan shida don ɗaukar nauyin karatun marayu a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Wani bawan Allah da bai so a bayyana sunan shi ba ya ware Naira milliyan shoda (6,000.000:00) domin daukar nnauyin karatun marayu da ke ƙarƙashin kulawar gidauniyar marayun ƙungiyar Mar’atusaliha Widows And Orphans Initiatiɓe da ke garin Argungu a jihar Kebbi.

Shugabar ƙungiyar Mar’atusaliha a Masarautar Kabin Argungu Hajiya Mariya Muhammad Mera ce ta bayyana haka a yayin da ta ke zantawa da wakilin Blueprint Manhaja a garin Argungu.

Ta bayyana cewa mutumin ya bayyana cewa ya kawo wannan tallafin ne saboda Allah don taimakawa marayun da ke ƙarƙashin kulawar wannan ƙungiyar a matsayin sadaka saboda Allah a yayin wata ziyarar bazata da ya kai gidan marayun.

Hajiya Mariya Mera ta ce ba tare da ɓata lokaci ba marayun za su soma amfana da wannan sadaka tun daga matakin karatu na ƙananan Sakandare (JSS) har zuwa kammala karatun sakandare na (SS).

Shugabar ta gode wa wannan bawan Allah tare da yi masa addu’ar samun sakamako na alheri daga Allah.

Ta kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan bawan Allah wajen ayyukan alkhairi na kyautata rayuwar marasa galihu domin samun babban rabo ranar lahira.

By ukarofi