Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin saukar da hauhawar farashi, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sauke hauhawar farashin kayayyaki zuwa ƙaramin mataki ga ‘yan Nijeriya, kamar yadda Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana.

Onanuga ya faɗi haka ne yayin da yake sanar da matakan da gwamnatin ta samar domin tallafa wa ‘yan ƙasa a daidai lokacin da ake fuskantar tsadar farashin fetur a matakin duniya. Farashin fetur dai ya yi tashin gwauron-zabi ne a sakamakon rufe mashigar Hormuz da ke yankin Gabas ta Tsakiya bisa rikicin Amurka da Iran.

Da fari, a ranar Alhamis ne Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattali, Taiwo Oyedele ya sanar da cewa za a riƙa siyar da fetur a farashi mai rangwame na tsawon kwana 30 a gidajen man NNPCL. Duk da cewa ministan ya bayyana ƙarara cewa hakan ba ya nufin za a dawo da tallafin fetur, ‘yan Nijeriya da dama musamman a kafafen sada zumunta, sun bayyana hakan a matsayin samar da tallafi ga man.

A sanarwarsa, Onanuga ya ce, Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya amince da haƙura da girman ribarsa ta siyar wa masu amfanin yau da kullum ta yadda za a riƙa siyar wa ‘yan Nijeriya a wani farashi domin rage raɗaɗin tasirin farashin ɗanyen mai a matakin duniya da samar da sauƙi ga al’ummar Nijeriya.

Ya bayyana cewa, za a yi hakan ne na tsawon wata guda, sannan wannan na nufin idan NNPCL ta samu farashin saukewa akan N1,300, to za ta riƙa siyar da shi akan haka musamman ga motocin ‘yan kasuwa.

Wannan mataki, wanda ya samu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu, na daga cikin matakan da Minista Taiwo Oyedele ya sanar a ranar, yana mai kira ga sauran manyan ‘yan kasuwa da su bi sawon NNPCL wajen samar da rangwame ga ‘yan ƙasa duba da cewa tashin farashin ba a tsammanin ya ɗauki tsawon lokaci.

By Babaji

Leave a Reply