Gwamnatin Tarayya na shirin gaggauta samar da gidaje yayin da Minista Darma ya ziyarci na rukunin 1,500 a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta sabunta muradinta na hanzarta samar da gidaje a sassan ƙasar nan domin inganta walwalar al’ummar ƙasa a fannin zamantakewa.

Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayyar Nijeriya, Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya bayyana haka yayin da ya ziyarci wani aikin gina gidaje na Renewed Hope City a Jihar Kano don samar da gidaje masu rahusa ga ‘yan ƙasa ta alaƙar ɗaiɗaikun mutane da gwamnati.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara wani rukunin gidaje guda 1,500 da ake ginawa a Kano, wanda ake sa ran zai ɗauki aƙalla mutane 6,000 yayin da aka kammala.

Ya kuma bayyana gamsuwa da matakin ci-gabam aikin, inda ya yaba wa abokan aiki da na aiwatarwa bisa ƙoƙarinsu akan al’amarin, yana mai kira da su ƙara ƙaimi wajen cika dukkan ƙa’idar da aka samar.

Haka kuma, Ministan ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya ta cigaba da samar da gidaje masu araha da ingantattun ababen more rayuwa ga ‘yan Nijeriya, yana mai cewa ayyukan na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta rayukan al’umma da samar da ci-gaba mai ɗorewa a ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply