Daga AISHA ASAS
(Ci gaba daga makon jiya)
Baya ga wannan, akwai wasu gwaje-gwaje da suka shafi lafiyar jiki gaba ɗaya waɗanda ya kamata a kula da su kafin aure.
Cutar hanta irin su hepatitis, alal misali, na iya wucewa daga mutum zuwa mutum ko daga uwa zuwa jariri. Haka kuma akwai cututtukan da ake ɗauka a matsayin “ƙanana” amma suke da babbar illa ga jarirai, kamar wasu cututtukan da mace za ta iya kamuwa da su ba tare da ta sani ba, amma su shafi jaririn da take ɗauke da shi.
Haka kuma batun gwaje-gwajen hormones yana da muhimmanci, musamman ga waɗanda ke son sanin yanayin haihuwarsu. A wasu lokuta, ma’aurata kan shiga damuwa bayan aure saboda jinkirin samun haihuwa, alhali akwai wasu matsaloli da za a iya gano su tun da wuri a gyara ko a shirya musu mafita.
Masana a fannin lafiya sun sha jaddada cewa, aure ba kawai haɗuwar zuciya ba ce. Tsari ne mai ɗauke da alhaki, wanda ke buƙatar cikakken shiri na ilimi da fahimta. Wani likita ya taɓa bayyana cewa, mafi yawan matsalolin da suke gani bayan aure, musamman na haihuwa, suna da alaƙa da abubuwan da za a iya gano su tun kafin aure amma aka yi watsi da su.
Abinda wannan darasin na wannan mako ke haskawa shi ne mu fahimci cewa, rashin sani ba kariya ba ne. A maimakon haka, wani lokaci shi ne tushen matsala. Mutane da dama suna tsoron yin cikakken gwaji saboda tsoron abin da za su gani, ko kuma saboda suna ganin hakan na iya kawo cikas ga shirin aure ko yin sa baki ɗaya. Amma gaskiyar magana ita ce, abin da ake gudu, shi ne yake biyo baya idan ba a fuskance shi da wuri ba.
Rayuwar aure tana ɗauke da buri na samun farin ciki, haihuwa, da gina zuri’a mai ƙoshin lafiya. Amma wannan buri ba zai tabbata ba idan aka gina shi a kan rashin cikakken sani. Yaron da za a haifa ba shi da laifi a kuskuren da aka yi kafin zuwansa duniya.
Wannan shi ne abin da ya kamata ya motsa zukatan matasa da iyaye su ɗauki wannan batu da muhimmanci fiye da yadda ake yi a yanzu.
A ƙarshe, darasin da ke nan shi ne: gwajin jini kafin aure ba wai kawai al’ada ba ce ko sharadi na coci ko asibiti. Wani muhimmin mataki ne na kare rayuwa ta ma’aurata da kuma ta ‘ya’yansu. Kuma wannan kariya ba za ta cika ba sai an faɗaɗa tunani fiye da gwajin genotype da kanjamau.
Aure na buƙatar soyayya, amma fiye da haka, yana buƙatar ilimi. Kuma ilimin da ba a nema ba, ba ya kare mutum daga sakamakon da zai zo.
